Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-13 17:54:14    
Wasu labarun jihar Tibet da jihar Xinjiang masu cin gashin kansu

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko dai ga wasu labaru game da jihar Tibet.

Labarin farko shi ne jihar Tibet tana samun cigaban tattalin arziki cikin sauri.

A cikin farkon rabin shekarar da muke ciki, jimlar kudaden samar da kayayyaki na jihar Tibet ta kai kudin Renminbi yuan fiye da biliyan 14, wato ya karu da kashi 15 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Wannan kuma ita ce karuwa mafi sauri da jihar ta samu a cikin shekaru 10 da suka wuce.

A ran 23 ga wata, lokacin da Jin Shixun, direktan kwamitin yin gyare-gyare da ci gaban jihar Tibet mai cin gashin kanta yake bayar da rahoto a gun taron zaunannen kwamitin majalisar dokokin jihar Tibet, ya ce, a sakamakon kyautatuwar ayyukan yau da kullu, musamman bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet, an samu kyakkyawar damar raya sana'o'in ba da hidima, musamman sana'ar yawon shakatawa a jihar. Mr. Jin ya ce, a cikin farkon rabin shekarar da muke ciki, yawan masu yawon shakatawa da suka kai ziyara a jihar Tibet ya kai fiye da miliyan 1 da dubu dari 1. A waje daya, bunkasuwar sana'ar yawon shakatawa tana yin kyakkyawan tasiri ga bunkasuwar sana'o'in abinci da cinikin kayan masarufi da dai makamatansu. Jimlar kudaden da aka samu daga cinikin kayan masarufi ya kai kudin Renminbi yuan biliyan 5.2.

Wani labari daban shi ne za a hana hako ma'aidinan mercury da arsenic da zinariya da kwal a jihar Tibet.

Bisa shirin hako ma'adinai na jihar Tibet da ake tsara, za a hana hako mercury da arsenic da kwal da zinariya a jihar domin kiyaye muhallin jihar.

A kwanan baya, Wang Baosheng, direktan hukumar kasa da albarkatu ta jihar Tibet mai cin gashin kanta ya gaya wa manema labaru cewa, ko da yake, jihar Tibet tana da wadatattun ma'adinan arsenic da zinariya, amma an riga an hana hako su domin kiyaye muhallin jihar.

An bayyana cewa, idan aka hako albarkatun mercury da arsenic, za a gurbata ruwa, idan aka hako kwal, za a lalata fadama. A waje daya, idan aka hako zinariya, za a taba filayen ciyayi da koguna na jihar.

Wang Baosheng ya kara da cewa, gwamnatin jihar Tibet za ta bayar da tsarin samar da kudin alkawarin mayar da muhallin wuraren da aka haka albarkatun kasa a karshen shekarar da muke ciki domin kara kiyayewa da raya masana'antun albarkatun kasa. Dole ne masu hako albarkatun kasa su sauke nauyin mayar da muhallin wuraren da aka hako albarkatun kasa da ke bisa wuyansu. Idan ba su iya sauke nauyinsu ba, za a yi amfani da kudin alkawarin da ya samar domin mayar da muhallin wuraren da aka hako albarkatun kasa.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa yanzu an riga an gano albarkatun kasa iri iri da yawansu ya kai fiye da dari 1 a jihar Tibet.

Labarin karshe shi ne jihar Xinjiang tana mai da hankali wajen horar da malamai 'yan kananan kabilu

Tun daga shekarar 2003, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da gwamnatin jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta sun riga sun zuba kudaden da yawansu ya kai kudin Renminbi yuan miliyan 130 wajen horar da malamai 'yan kananan kabilu fiye da dubu 10 domin makarantun firamare da na sakandare na kananan kabilun da ke zama a jihar domin kyautata ingancin daliban makarantun firamare da na sakandare na kananan kabilu na jihar.

An samu wannan labari ne a gun taron kara wa juna sani kan "tallafawa shirin horar da malamai na makarantun firamare da na sakandare na jihar Xinjiang da ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ke yi" da aka shirya a birnin Urumqi na jihar a ran 6 ga wata. (Sanusi Chen)