Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-10 17:52:54    
Kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa na mai da hankali kan ayyukan share fagen taron wasannin Olympic na Beijing

cri

Aminai 'yan Afrika, lokaci na gudu da sauri fa. Amma idan ba a manta ba, ana iya waiwayen halin da ake ciki a shekarar 2001 wato lokacin da gwamnatin birnin Beijing na kasar Sin ta samu izinin gudanar da taron wasannin Olympic na shekarar 2008. Ga shi, tun daga yanzu dai, ayyukan share fagen wannan gagarumin taron sun shiga matakin karshe. Kwanakin baya, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya yi cikakken zaman taronsa na 119 a kasar Guatemala, inda aka kada kuri'un zaben birnin Sochi na kasar Rasha a matsayin birni da zai gudanar da taron wasannin Olympic na yanayin sanyi a shekarar 2014. Ban da wannan kuma, an saurari rahotanni kan ci gaban ayyukan share fagen wasu tarurrukan wasannin Olympic na nan gaba, wadanda masu shirya tarurrukan wasannin suka gabatar. Wannan shi ma ya kasance karo na karshe ne da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya gabatar da rahoto ga dukannin mambobin kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa kafin a bude taron wasannin Olympic na shekarar 2008. To, me ya fi janyo hankulan mambobi sama da 100 na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa game da ayyukan share fage na shekarar karshe da gwamnatin Beijing take yi?

Aminai 'yan Afrika, mun yi farin ciki matuka da gaya muku cewa, har kullum gwamnatin birnin Beijing na gudanar da ayyukan share fage lami-lafiya tun bayan da ta samu izini shirya taron wasannin Olympic na yanayin zafi na shekarar 2008 a shekarar 2001. Gwamnatin birnin Beijing ta shirya wani rahoto mai kyau kan ayyukan share fage ,wanda ta gabatar wa cikakken zama na taron wasannin Olympic na kasa da kasa a wannan gami.

Mr. Wang Wei, mataimakin shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing kuma babban sakataren kwamitin ya yi bayani kan rahoton cewa : ' Muhimman abubuwan dake cikin rahoton sun hada da ayyukan gina filaye da dakunan wasanni, da shirin bai wa juna wutar yula, da aikin share fagen bikin bude taron wasannin Olympic da kuma na rufe shi da dai sauransu. Nufinmu shi ne barin mambobin kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa su kara fahimtar taron wasannin Olympic na Beijing '.

Mr. Wang Wei ya kuma fayyace cewa, dukkan mambobin kwamitin sun gamsu sosai da sauraron rahoto kan ayyukan share fage da ake yi a Beijing. Daraktan zartaswa na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa Mr. Gilbert Felli ya ce : ' Rahoton yana da kyau yana da kyau. Amma wasu fannoni na ayyukan share fagen taron wasannin Olympic na Beijing sun fi janyo hankulan mambobin kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa, musamman ma a game da batun kiyaye muhalli. Mambobi da dama dake cikin kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa 'yan wasa ne a da. Babu tantama, sun gane tasirin da ingancin iskar sararin samaniya yakan yi ga 'yan wasa.

Mr. Wu Jingguo, mamban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa daga Taibei ta kasar Sin ya furta cewa : ' Lallai abun ya fi janyo hankulan mutane. Kowa ya sani, yanzu ana namijin kokari wajen kyautata muhallin Beijing, musamman ma ingancin iskar sararin samaniya. Nan gaba, za a iya kafa tashoshin sa ido da dama domin bullo da rahotanni kan ingancin iskar sararin samaniya'.

Mr. Felli shi ma ya fadi cewa, mambobin kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa sun san cewa, lallai yanayin muhalli na Beijing ya yi manyan sauye-sauye bayan da ta yi nasarar samun izinin shirya taron wasannin Olympic ; haka kuma sun san cewa gwamnatin birnin Beijing ta yi ayyuka da yawa. Dukansu sun ce, kasar Sin ta samu bunkasuwa da saurin gaske.

Mr. Richard Pound, mamban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa daga kasar Canada ya tofa albarkacin bakinsa kan batun yaki da shan maganin sa kuzari a gun taron, inda ya furta cewa : ' A gaban kasashen

Duk duniya, wajibi ne mu bada tabbaci ga gwamnatin Beijing wajen aiwatar da ayyuka mafi girma na gwajin maganin sa kuzari da kuma shirin horaswa mafi girma na yaki da shan maganin sa kuzari. A kan maganar yaki da shan maganin sa kuzari, duk kowace kasa a duniya ba za iya guje wa hadarurruka ba. Saboda haka, abun ya zama babban nauyi ne dake bisa wuyanmu na gudanar da harkar yaki da shan maganin sa kuzari kamar yadda ya kamata.''

Ban da wadannan kuma, gasar jarrabawa da za a nan gaba kadan, da shirin sayar da tikitocin shiga kallon taron wasannin Olympic, da shirye-shiryen gudanar da bukukuwan budewa da kuma rufe taron wasannin Olympic na Beijing da dai sauransu, batutuwa ne da dimbin mambobin kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa suka fi mai da hankali a kai.

Mr. Juan Antonio Samaranchi, tsohon shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa kuma shugaba mai daukaka na tsawon rai da rai na kwamitin ya tabbatar da cewa : ' Ina cike da kyakkyawan imani ga kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing. A cikin shekara guda mai kamawa, za a iya warware dukkan maganganu da kyau ciki har da maganar gurbacewar iska ta sararin samaniya'. ( Sani Wang )