Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-08 16:39:11    
Yin saye-saye a shagunan da ke titin Barkhor a birnin Lhasa

cri

A tsohon titin Barkhor da ke birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, akwai shaguna masu sigogin musamman da yawa. Yau ma bari mu kai ziyara tare.

Titin Barkhor mai siffar da'ira yana tsohon bangare na brinin Lhasa, wani sunansa daban shi ne titin Bajiao, tsawonsa ya kai mita dubu 1 ko fiye. Tarihinsa ya wuce shekaru dubu 1 da dari 3. An shimfida wannan titi da duwatsun da aka nika su da hannu. Ko da yake ba shi da fadi sosai, amma shi ne wurin da aka fi samun mutane masu kaiwa da kawowa a Lhasa a ko wace rana.

A kan titin Barkhor, kantuna da shaguna masu dimbin yawa suna yin ciniki, dimbin mutane suna kaiwa da kawowa. 'Yan kasuwa marasa rumfuna fiye da dubu daya suna sayar da abubuwa a titin. A cikin shaguna da kantunan da ke gefunan titin, ana sayar da tufafin 'yan kabilar Tibet, da wukaken da 'yan kabilar Tibet suka kera, da kayayyakin da ke da nasaba da addini iri daban daban, ban da wanan kuma, ana sayar da kayayyakin koli daban daban da aka shigo da su daga kasashen Indiya da Nepal. Wasu daga cikin wadannan shaguna da kantuna su ne Musulmai da 'yan kaka gida na Nepal suke tafiyar da su, wadanda suka yi shekaru da yawa suna zama a Lhasa. Ga misali, a arewacin titin Barkhor, wani kanti mai suna Syamu Kapu ya rataya alluna 3 na zamani daban daban a kofarsa domin nuna cewa, tarihin kantin na da tsawon shekaru fiye da dari. Shigowar mutane cikin kantin ke da wuya, sai suka ga wani tsohon hoto da ke kan teburin a kusa da kofar, inda wani namiji ya sa tufafin irin kabilun kasashen Yammacin Asiya tare da wani farar hula a kansa. Mai kantin malam Ratna ya yi bayani cewa, wannan namiji kakansa ne, ya zo Tibet daga Nepal domin yin ciniki a farkon karnin da ya gabata. Ya ce, 'Shi ne Syamu Kapu, kakana. A farkon lokacin da ya yi ciniki a Lhasa, 'yan kabilar Tibet na wurin ba su iya kiran sunansa na anihi ba, amma saboda ya sa fararen tufafi tare da wata farar hula a kansa, shi ya sa mazaunan wurin su kan kira shi Syamu Kapu, wato hula mai launin fari. Ta haka ne aka sami sunan wannan kanti.'

Kantin Syamu Kapu tsohon kanti ne a kan titin Barkhor, yana sayar da mutum-mutumin Buddha da kayayyakin fasaha irin na gargajiya, wadanda aka kera da karfe iri-iri a zamani daban daban. Dukkansu an kera a Nepal.

Titin Barkhor titin kasuwanci ne mafi wadata a Lhasa, wanda yake nuna al'adun gargajiya na kabilar Tibet, shi ya sa akwai kantuna da shaguna da yawa da ke sayar da kayayyakin fasaha irin na kabilar Tibet, yawancinsu suna sayar da zane-zanen Tangkar na Tibet da kuma kafet din da 'yan kabilar Tibet suka saka da hannu. Zane-zanen Tangkar na Tibet na gargajiya irin zane-zane ne na addini da aka nannade, bayan da aka yi musu ado tare da siliki masu launuka daban daban, an rataya su domin yin ibada. Haka kuma su ne irin fasahar zane-zane mai sigar musamman a cikin al'adar kabilar Tibet. Kantunan sayar da zane-zanen Tangkar suna jawo dimbin masu yawon shakatawa na gida da na waje. Malama An Meihua, wata budurwa daga kasar New Zealand, yanzu tana karatu a Jami'ar Beijing. Sunan da ta nada wa kanta ya nuna al'adun kasar Sin sosai, haka kuma, ta iya Sinanci da harshen kabilar Tibet sosai. Bayan da An Meihua ta ziyarci kantunan sayar da kayayyakin fasaha, wadannan kyawawan zane-zanen Tangkar sun janyo hankalinta kwarai. Ta ce, 'Duk al'adu na da ban sha'awa a gare ni, sa'an nan kuma, sun sha bamban da juna. Ko da yake wasu al'adu sun sha bamban da juna a fannoni daban daban a fuska, amma a zahiri, a ganina, al'adunmu iri daya ne.'

A ko wace rana da misalin karfe 9 da safe, masu yawon shakatawa da suka fito daga ko ina a duniya su kan taru a titin Barkhor. Kantuna da shaguna cike suke da kayayyakin fasaha iri daban daban da masu kananan sana'o'i suka kera, da kafet masu launuka daban daban da aka saka da hannu, da hulunan musamman irin na birnin Rikaze, da kwanonin katako, da abubuwan hannu da na wuya da aka yi da karafa iri daban daban, dukansu sun jawo sha'awar mutane sosai. Da dare kuwa, titin nan ya fi kyan gani. A ko wane dare, mutane suna yawo a wajen, kantuna da shaguna suna ci gaba da bude kofofinsu. Kide-kide masu dadin ji da ihun mutane domin sayar da abubuwa da kuma kamshin abinci dukkansu sun sanya mutane su manta da komawa gida. Malam Tsering Wangqing, wani mai kanti a titin Barkhor, ya bayyana ra'ayinsa kan wannan titi, 'Mutane daban daban suna kaiwa da kawowa a kan titin Bajiao wato Barkhor. A gaskiya kuma titin Barkhor na Lhasa wuri ne da aka fi samun mutane na kasashe daban daban. Masu yawon shakatawa na wurare daban daban na duniya sun ziyarci titinmu, inda suke iya fahimtar al'adun kabilar Tibet, a sa'i daya kuma, su kan ji kamar suna gida.'