Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-08 16:32:59    
Cikakken tarihin majalisar dinkin duniya

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Musa Sama'ila, mazaunin birnin Jalingo da ke jihar Taraba, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya turo mana a kwanan baya, malam Musa Sama'ila ya ce, ina so ku ba ni cikakken tarihin majalisar dinkin duniya a filinku na "amsoshin wasikunku", shin yaushe ne aka kafa majalisar, kuma mambobi nawa take da su a halin yanzu. Sa'an nan, wadanne hukumomi ne suke kasancewa cikin majalisar.

MDD ta kafu ne a lokacin da aka cimma nasarar yakin duniya na biyu. A ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 1942, wakilan kasashe 26, ciki har da na Sin da Amurka da Birtaniya da Rasha da sauransu, wadanda ke yakar dakaru na kasashen Jamus da Italiya da Japan, sun bayar da sanarwar kafa majalisar dinkin duniya a birnin Washington. Daga baya, a ranar 25 ga watan Afril na shekarar 1945, wakilan da suka zo daga kasashe 50 sun yi taro a birnin San Francisco na kasar Amurka. A ranar 26 ga watan Yuni na shekarar, wakilan sun rattaba hannu a kan tsarin dokokin MDD, daga bisani, Poland ita ma ta sa hannunta. A ranar 24 ga watan Oktoba na shekarar, tsarin dokokin ya fara aiki, kuma UN, wato majalisar dinkin duniya ta kafu a hukunce. A shekarar 1947, MDD ta kuma tsai da ranar 24 ga watan Oktoba na kowace shekara a matsayin ranar MDD.

A hakika, idan wata kasa tana son shiga MDD, dole ne ta gabatar da takardar bayyana rokonta, kuma ta sanar da amincewa da nauyin da tsarin dokokin MDD ya dora wa mambobinta, sa'an nan, idan fiye da kashi 2 daga cikin uku na mambobin MDD sun nuna amincewa ga rokon, to, za a iya shigar da kasar cikin MDD. Kawo ranar 28 ga watan Yuni na shekarar 2006 da ta gabata, yawan kasashe mambobin MDD ya riga ya kai 192, kuma daga cikinsu, 39 sun zo ne daga nahiyar Asiya, 53 kasashe ne na Afirka, bayan haka, akwai kuma mambobi 28 da suka kasance kasashe na gabashin Turai da na kungiyar kasashe masu 'yancin kai na tsohuwar Tarayyar Soviet tare kuma da 23 na yammacin Turai, a yayin da mambobi 33 suka zo daga Latin Amurka da kuma 16 da suka zo daga arewacin nahiyar Amurka da kuma nahiyar Oceania.

Muhimman hukumomin MDD sun hada da babban taron MDD da kwamitin sulhu da kwamitin kula da harkokin tattalin arziki da zaman al'umma da majalisar amintattu da kotun duniya da kuma babban ofishin MDD.

Babban taron MDD yana samun halarta daga dukan mambobin MDD, kuma ya kan kira zaunannen taronsa a watan Satumba na kowace shekara. Sa'an nan, kwamitin sulhu shi ma wata muhimmiyar hukuma da ke cikin MDD. Kamar yadda kowa ya sani, kasashen Sin da Faransa da Rasha da Birtaniya da Amurka suna da kujerun dindindin a kwamitin sulhu, bayan haka, a kan kuma zabi kasashe 10 daga shiyyoyi daban daban don su zama kasashen da ba na dindindin ba a kwamitin sulhu. Bisa tsarin dokokin MDD, kwamitin sulhu na da babban nauyi ta fuskar kiyaye zaman lafiya da kuma tsaro a duniya. Sai kuma babban ofishin MDD wanda ke kunshe da babban sakataren MDD da kuma ma'aikatan majalisar, yana bauta wa MDD da kuma hukumomin da ke karkashin jagorancinta tare kuma da aiwatar da shirye-shirye da manufofin da hukumomin suka tsara. Babban sakataren MDD shi ne shugaban koli na MDD. Mr.Ban Ki-moon, babban sakatare mai ci yanzu na MDD, shi ya kasance babban sakatare na takwas a tarihin MDD. Bayan wadannan, MDD ta kuma kafa dimbin sauran hukumomi bisa bukatunta.

A shekaru da dama da suka wuce, MDD ta yi ta bunkasa kuma ta bayar da babban taimako a wajen tabbatar da zaman lafiya da albarka ga dan Adam. Nasarorin da ta samu ta fuskokin 'yantar da jama'ar duniya da kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya da sa kaimi ga cigaban tattalin arziki da zaman al'umma sun burge kowa. Tun daga shekarar 1948 har zuwa yanzu, gaba daya ne kwamitin sulhu na MDD ya ba da iznin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya da suka kai sama da 60. Ban da wannan, daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya har zuwa yarjejeniyar amfani da sararin samaniya domin zaman lafiya, MDD ta kuma tsara darurruwan yarjejeniyoyin duniya, yanzu MDD ta riga ta zamanto kungiyar duniya mafi fada a ji da ke tsakanin gwamnatocin kasashe daban daban.(Lubabatu)