Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-08 08:25:32    
`Yan wasan kwallon gora na kasar Sin sun shiga babbar kungiyar wasan kwallon gora ta kasar Amurka

cri

Masu sauraro,kamar yadda kuka sani,wasan kwallon gora shi ne wasa mai ban sha`awa,ya samu karbuwa sosai daga duk fannoni,musamman a kasar Amurka da ta Japan da ta Korea ta kudu da kuma wasu kasashen dake Latin Amurka.A wadannan wurare,kusan kowa ya san taurarin `yan wasan kwallon gora kamarsu Babe Ruth da Reggie Jackson da sauransu.Amma a kasar Sin,an fara wasan kwallon gora ba da dadewa ba,matsayin wasan na kasar Sin bai kai na wasu kasashe ba.Duk da haka,ana yin kokari,kawo yanzu,halin ya canja wato ya samu kyautatuwa a kai a kai.A watan Yuli na wannan shekarar da muke ciki,`yan wasan kwallon gora na kasar Sin hudu wadanda suka hada da Liu Kai da Zhang Zhengwang da Wang Wei da kuma Jia Yubing bi da bi ne sun daddale yarjejeniya da kungiyar New York Yankee da kungiyar Seatle Mariner na kasar Amurka wato sun shiga babbar kungiyar wasan kwallon gora ta kasar Amurka.Wannan ya jawo hankulan mutanen duniya.Saboda haka,wakilinmu ya ziyarci Wang Wei da Jia Yubing don jin ta bakinsu.

Wang Wei yana da shekaru 29 da haihuwa,yanzu shi ne muhimmin `dan wasa na kungiyar damisa ta Beijing da kungiyar kasar Sin,kungiyar damisa ta Beijing ta taba samu zama ta farko sau biyu a gun babbar gasar wasan kwallon gora ta kasar Sin a karkashin jagorancinsa.Amma,a shekarar 2006,Wang Wei ya yi suna sosai saboda ya yi wasan gudun gida (home run) mai kyau a gun gasar shahararrun `yan wasan kwallon gora ta duk duniya wadda matsayinta ya fi koli a duniya.Shi ya sa kungiyar Seatle Mariner ta kasar Amurka ta gayyace shi da ya shiga kungiyarta.Wang Wei ya ji dadi kan wannan kuma ya yi farin ciki kwarai da gaske.Ya ce:  `Shiga babbar kungiyar wasan kwallon gora ta kasar Amurka shi ne mafarkina,kuma shi ne mafarki na kowanen `dan wasan kwallon gora,ana iya cewa,na samu wani izni mai kyau,ko shakka babu zan yi amfani da shi,zan yi kokari.`

Jia Yubing shi ma ya shiga kungiyar Seatle Mariner ta kasar Amurka,a wannan shekara,yana da shekaru 24 da haihuwa kawai,amma ya riga ya fara wasan kwallon gora da shekaru 15,fasahar wasansa tana da kyau,ya taba zama `sarkin wasan gudun gida wato `home run` `a gun babbar gasar wasan kwallon gora ta kasar Sin.Yayin da Jia Yubing ya ji labari game da zai tafi kasar Amurka domin wasan kwallon gora,bai yi farin ciki kamar yadda Wang Wei ya yi ba.Dalilin da ya sa haka shi ne domin Jia Yubing ya san ba zai samu iznin shiga babbar gasa ba sai dai ya yi matukar kokari,saboda a kungiyoyin sana`a ta babbar kungiyar wasan kwallon gora ta kasar Amurka,fiffitattun `yan wasa sun yi yawan gaske.Jia Yubing ya ce:  `Na san matsayina bai kai na sauran taurarin `yan wasa ba,musamman wajen karfin jiki da kuma fasaha.Amma zan yi iyakacin kokari saboda na samu wannan izni mai kyau,kuma ina fatan zan shiga babbar gasa ta babbar kungiyar wasan kwallon gora ta kasar Amurka bayan kokarin da na yi.`

A shekarar 2005,kwamitin wasannin Olimpic na duniya ya tsai da kuduri cewa,ba za a shirya gasar wasan kwallon gora a gun taron wasannin Olimpic na shekarar 2012 ba.Amma a watan Yuli na wannan shekara,a gun cikakken taro na 119 da kwamitin wasannin Olimpic na duniya ya yi a birnin Guatemala na kasar Guatemala,an zartas da wani shirin yin gyare-gyare,inda aka tsai da cewa,a gun taron wasannin Olimpic na shekarar 2020,za a shirya wasanni 25,kuma tun daga wannan taron wasannin Olimpic ne,za a kara wasanni 3 na wucin gadi.Ko wasan kwallon gora zai sake shiga taron wasannin Olimpic?Ba a san sakamako ba yanzu,amma yana da izni.Game da wannan,Wang Wei da Jia Yubing sun bayyana cewa za su yi kokari saboda suna fatan kungiyar wasan kwallon gora ta kasar Sin za ta samu sabon ci gaba a gun taron wasannin Olimpic na Beijing da za a yi a shekarar 2008,kila ne gasar wasan kwallon gora ta taron wasannin Olimpic gasa ta karshe ce ta taron wasannin Olimpic.Jia Yubing ya ce: `Ina ganin cewa,idan ana so a samu sakamako mai kyau,dole ne dukkan `yan wasa su yi kokari tare,shi ya sa ya fi kyau dukkan `yan wasan kwallon gora na kungiyar kasar Sin su yi kokari tare,daga baya kuma matsayin kungiyar kasar Sin zai dada daguwa,a sakamakon haka,kungiyar kasar Sin za ta samu sakamako mai faranta ran mutane a shekarar 2008.`

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)