Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-07 18:45:34    
Kabarin Zhaojun a birnin Hohhot na jihar Mongolia ta Gida

cri

Birnin Hohhot yana tsakiyar jihar Mongolia ta Gida mai cin gashin kanta, shi ne kuma babban birnin wannan jiha. A bakin 'yan kabilar Mongolia, ma'anar Hohhot ita ce koren birni. Babban tsaunin Daqingshan da ake samun bishiyoyi da yawa a wajen ya kewaye wannan birni daga gefuna 3, wato daga arewa da gabas da kuma yamma.

Birnin Hohhot yana dogara da masana'antun samar da kayayyakin masakan ulu da kera injuna da samar da karfe da bakin karfe da magunguna da sarrafa sukari da kuma kayayyakin masarufi na zaman yau da kullum domin bunkasa kansa. Masu yawon shakatawa suna kaunar ziyarar gidan ibada na Lama na Dazhaosi da kabarin Zhaojun da kuma gidan ibada na Wutasi.

A cikin dukkan wadannan shahararrun wuraren yawon shakatawa da ke birnin Hohhot, kabarin Zhaojun da ke kudu maso yammacin birnin ya fi jawo masu yawon shakatawa. An gina wannan kabari ne domin tunawa da Wang Zhaojun. A shekarar 22 kafin haihuwar Annabi Isa A.S., Chanyu, sarkin daular Xiongnu ko kuma Hun, wadda wata daula ce mai karfi da makiyaya suka kafa, ya gabatar da rokon neman yin aure ga sarautar daular Han domin raya huldar abokantaka a tsakanin bangarorin 2. An zabi Wang Zhaojun saboda kyan ganinta. Wang Zhaojun ta je yanki karkara da Chanyu ke mulki, ta aure shi bisa son ranta, ta kuma kasance tare da jama'ar daular Xiongnu har tsawo rayuwarta.

Mutanen kasar Sin suna ta tunawa da Wang Zhaojun, saboda gudummowar da ta bayar wajen dinkuwar dukkan kabilun kasar Sin gaba daya. Sa'an nan kuma, sun mayar da ita a matsayin daya daga cikin mashahurran kyawawan mata 4 na zamanin da a kasar Sin.