A shekaru 60 na karnin da ya gabata, Zhang wanwen ya gama karatunsa daga jami'ar Fudan, wata shahararriyar jami'a ta kasar Sin. Daga baya kuma ya taba yin aiki na koyarwa a shiyyar kabilar Tibet mai cin gashin kai da ke kudancin lardin Gansu da kuma birnin Lanzhou, hedkwatar lardin. Bayan da Malam Zhang ya yi ritaya, ba ya son kashe lokacinsa wajen huta ba, yana ganin cewa, jikinsa yana da lafiya, shi ya sa ya kamata ya samar da taimako ga sauran mutane bisa fasahar da yake da ita, musamman ma ga 'yan makaranta masu fama da talauci, sabo da haka ya fara ba da lacca gare su bayan an tashi daga aji ba tare da karbar kudi ba.
Lokacin da wakilinmu ya ga Malam Zhang, yana bayar da lacca ga wasu yara. A cikin wani dakin da fadinsa ya kai murabba'in mita fiye da goma, yara hudu sun zauna tare don sauraron laccar da Malam Zhang ke bayar. Ko da yake gashin kan Zhang Wanwen fari ne, amma lokacin da yake tare da yara, har kullum ya kan ji farin ciki sosai.
Kullum Malam Zhang ya kan ba da lacca ga yara a kwanaki hudu da dare a ko wane mako. Domin yaran sun iya samun ilmi cikin sauki, ya haya wani daki a matsayin aji, sabo da haka wurin ya zama tamkar wata makaranta ga yara fiye da goma cikin dan lokaci kadan. Yawancin yaran da ke cikinsu suna fama da talauci, shi ya sa Malam Zhang ya ba su lacca ba tare da karbar ko kobo ba.
Dalilin da ya sa Malam Zhang ya fara tafiyar da wannan aiki shi ne sabo da wani lamarin da ya faru yau da shekaru 4 da suka gabata. A wancan lokaci, wani yara mai suna Wang Jie ya kan samu ilmi daga wajen Malam Zhang bayan ya tashi daga aji. Mahaifinsa ya riga mu gidan gaskiya, mahaifiyarsa tana yin aikin shara a cikin wani otel, kuma albashin da take samu a ko wane wata ya kai yuan daruruwa kawai, shi ya sa suna fama da talauci sosai. Wannan lamari ya burge Malam Zhang, kuma ya tsai da kudurin ba da lacca ga yara masu fama da talauci ba tare da karbar ko kobo ba. Malam Zhang ya gaya mana cewa,
"Na nuna tausayi sosai ga yara masu fama da talauci, dalilin ya sa haka shi ne sabo da na taba fama da talauci a lokacin yarantakata. Ban da wannan kuma yawan yara da suka zo gidana don samun ilmi ya yi kadan, shi ya sa idan an kara daya ko biyu, ba za su yi illa ga sauran yara ba. Ganin haka, na yi la'akari kan amincewa da yara masu fama da talauci da su zo gidana."
Domin kwanta da hankulan yara wajen karatu, a wasu lokuna Malam Zhang ya kan sayi abinci da kayayakin karatu gare su, sabo da haka yara masu yawa su kan kiransa kaka Zhang.
Kamar yadda Hausawa su kan ce, kamar yadda muka shuka, haka nan muka girba. Sabo da Malam Zhang yana da dabarun koyarwa iri daban daban, kuma ya samu sakamako mai kyau wajen koyarwa, shi ya sa yaran da suka yi karatu a nan sun samu ci gaba a bayyane, wasu dalibai kuma suna kan gaba a ciki azuzuwansu.
Da ma, Yujia wani yaro ne mai fitina, kuma ba safai ya kan ci jarrabawa ba. Amma Bayan shekaru biyu da ya je gidan Malam Zhang wajen karatu, ya samu babban ci gaba. Kuma ya gaya mana cewa,
"A da, makina wajen karatu ba shi da kyau, amma bayan da Malam Zhang ya ba ni lacca, na samu ci gaba sosai. Malam Zhang mutum ne mai kirki sosai, na taba ganin cewa, ya sayi abin sha da kuma abinci ga dalibai masu fama da talauci, kuma idan suka ji barci, to suna iya kwantawa a kan gadonsa don hutawa."
Lokacin da Malam Zhang ke ba da lacca ga yara, shi wani malami ne da ya cika bin ka'ida sosai. Amma lokacin da yake zama yau da kullum, shi wani kaka ne mai kirki. Ba kawai yaran suna iya samun ilmi da yawa daga wajensa ba, har ma suna iya koyon yadda ya kamata a bayar da gudummowarsa ga zamantakewar al'umma.
A kwanan nan, Malam Zhang ya tsara wani sabon shiri, wato daukar wasu daliban da ba su yi kokari wajen karatu ba, da kuma koyar musu dabarun karatu ba tare da karbar kudi ba domin su nuna sha'awa ga karatu. Ta haka Malam Zhang yana ta yin nazari a kan hanyar tafiyar da aikin koyarwa ba tare da karbar kudi ba, yana fatan zai iya samar da taimako ga yara masu yawa.
To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin ke nan. Muna fatan kun ji dadinsu, da haka a madadin Kande wadda ke fassara bayanin, Lawal nake cewa mako gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Kande Gao)
|