Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-06 21:22:09    
Jihar Tibet za ta bin hanyar neman bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba

cri

Barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Kananan kabilun kasar Sin. A cikin shirinmu na yau, da farko dai, za mu kawo muku wash labaru game da jihar Tibet kamar yadda muka saba yi a cikin wadannan makonnin da suka wuce. Labarin farko shi ne, jami'in gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta ya ce, tabbas ne jihar Tibet ba za ta bi hanyar neman bunkasuwa ta gurbata muhalli, sannan a sake tsabtace shi ba.

Bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet, batun yadda za a kiyaye muhallin jihar Tibet ya jawo hankulan duniya sosai. Game da wannan batu, Deng Xiaogang, mataimakin shugaban jihar Tibet mai cin gashin kanta ya gaya wa manema labaru a birnin Lhasa cewar, jihar Tibet ba za ta bi hanyar neman bunkasuwa ta gurbata muhalli, sannan a sake tsabtace shi ba.

Bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet, an kafa wani cikakken tsarin zirga-zirga, ciki har da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet da tsarin hanyoyin motoci da tsarin zirga-zirgar jiargen sama. Wadannan tsare-tsaren zirga-zirga sun zama sharadin shigar da kasuwannin jihar Tibet ciin kasuwannin duniya. Deng Xiaogang ya ce, lokacin da take kiyaye muhalli, jihar Tibet za ta kara raya da yin amfani da albarkatun kasa bisa shirin da aka tsara, kuma a farko dai za ta kara raya masana'antu wadanda ba za su gurbata muhalli ba da raya sana'o'in da ke bayyana halin musamman na tudun Qinghai-Tibet. A waje daya, za a kara kiyaye muhallin wuraren yawon shakatawa.

Wani labari daban shi ne ana dumamar yanayin Tibet

Bisa sakamakon nazari da cibiyar nazarin yanayin duniya ta jihar Tibet ta samu, an bayyana cewa, domin ana dumamar yanayin duniya, ana kuma dumamar yanayin jihar Tibet.

Wani babban injiniya na cibiyar nazarin yanayi ta jihar Tibet ya ce, bisa sakamakon da aka samu, yanayin jihar Tibet yana karuwa da centigrade 0.3 a cikin ko wadannen shekaru 10, wato a bayyane ne wannan ya fi sauri bisa na matsakaicin yawan yanayin kasar Sin ko na duniya. To, jama'a masu sauraro, yanzu ga labarin karshe na yau, wato a karo na uku ne jihar Tibet ta soma binciken abubuwan tarihi

A kwanan baya, jihar Tibet mai cin gashin kanta ta soma binciken abubuwan tarihi a tsanake a karo na 3.

Wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya samu wannan labari ne a gun bikin kaddamar da binciken da aka yi a birnin Lhasa a ran 12 ga wata. Mukasudin yin wannan bincike shi ne ana sanin halin da abubuwan tarihi suke ciki a jihar Tibet, da kafa tare da kyautata adadin da yake da nasaba da abubuwan tarihi na kasar Sin da na jihar Tibet da abubuwan da suke cikin shiyoyyin kananan gwamnatocin jihar. Sannan za a iya kafa da kyautata matakan kiyaye abubuwan tarihi.

Wani jami'in hukumar harkokin abubuwan tarihi ta jihar Tibet ya bayyana cewa, za a yi wannan bincike ne har na tsawon shekaru 5. (Sanusi Chen)