Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-06 17:51:59    
Beijing na shirya taron wasannin Olympic yadda ya kamata

cri

Ran 8 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki rana ce da ta rage sauran shekara guda da bude taron wasannin Olympic a birnin Beijing a shekarar 2008. A wannan muhimmiyar rana, babu tantama ci gaban ayyukan shirye-shiryen taron wasannin Olympic na Beijing ya jawo hankulan duk kasashen duniya. Yau jami'an kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing sun bayyana cewa, yanzu Beijing tana share fage kan wannan muhimmin taron wasannin motsa jiki bisa shirin da aka tsara, ta kuma tabbatar da makasudi na matakai daban daban a daidai lokacin da aka tsara.

Ran 6 ga wata, a gun taron manema labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya, malam Wang Wei da Jiang Xiaoyu, mataimakan shugabannin zartaswa na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing sun yi karin bayani kan sabon ci gaban ayyukan shirye-shirye. Wang Wei ya ce,'Mun yi alkawari a gaban duk duniya a tsanake cewa, za mu shirya taron wasannin Olympic na matsayin koli mai sigar musamman a shekarar 2008, hakan bukata da kuma buri ne da gwamnatinmu da jama'armu suke bayar. Ayyukan shirya taron wasannin Olympic na Beijing suna samun jagoranci da goyi baya daga kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa, suna kuma jawo hankulan hukumomi na matakai daban daban na kasar Sin sosai, sa'an nan kuma, suna jawo hankulan duk jama'ar Sin da rukunoni daban daban na zaman al'ummar Sin da kuma samun cikakken taimako daga wajensu. A galibi dai, Beijing na shirya taron wasannin Olympic bisa shirin da aka tsara yadda ya kamata.'

Wadannan mataimakan shugabanni 2 sun yi karin bayanin cewa, za a yi amfani da filaye da dakunan wasa guda 37 da irin na horaswa guda 56 domin taron wasannin Olympic na Beijing. Ya zuwa yanzu dai, an kammala gina sabbin filaye da dakunan wasa guda 12, ana yi musu ado da kuma ajiye injunan wutar lantarki. Baya ga filin wasa na kasar Sin, wanda za a kammala gina shi a farkon shekara mai zuwa, saboda ayyukan bikin bude taron, za a kammala gina dukkan sauran filaye da dakunan wasa a karshen wannan shekara.

Sun ci gaba da cewa, ana gudanar da ayyukan shiryawa a sauran fannoni domin taron wasannin Olympic na Beijing lami lafiya.

Yin taron wasannin Olympic na matsayin koli mai sigar musamman a shekara mai zuwa makasudi ne da Beijing ta tsara. Ayyukan shirya wannan muhimmin taron wasannin motsa jiki sun sami goyi baya daga zaman al'ummar Sin da kuma jama'ar Sin, wadanda suke kuma shiga a ciki. Malam Jiang ya ce,'Taron wasannin Olympic wata kyakkyawar dama ce a tarihi. Shirya irin wannan taron wasannin motsa jiki na sa kaimi ga Beijing a fannonin ci gaban birnin da bunkasuwar tattalin arziki da raya birnin da kyautatuwar manyan ayyuka, ban da wannan kuma yana zabura daga matsayin Beijing ta fuskar tafiyar da harkokin birni ta hanyar zamani.'

A lokacin da ake shirya taron wasannin Olympic na Beijing, batun muhalli na ta jawo hankulan mutane. Wang Wei ya nuna cewa, tun daga shekarar 1998, hukumar Beijing ta soma kyautata iska. A cikin shekaru 8 da suka wuce, ingancin iskar Beijing na sami kyautatuwa sosai. Ya ce,'A lokacin taron wasannin Olympic a shekara mai zuwa, tabbas ne ingancin iska zai yi kyau sosai a Beijing. Wannan na da muhimmanci sosai wajen bikin bude taron, haka kuma yana da muhimmanci ainun ga lafiyar 'yan wasa da gasannin da za su yi da kuma lafiyar duk 'yan birnin.'

Saboda ana share fage kan taron wasannin Olympic yadda ya kamata, shi ya sa Jiang Xiaoyu ya bayyana cike da imani cewa, a watan Agusta mai zuwa, tabbas ne Beijing zai share fage daga dukkan fannoni, yana maraba da bakinmu na wurare daban daban na duniya su shiga taron wasannin Olympic na Beijing. Ya ce,'Tabbas ne za mu yi maraba da bakinmu na wurare daban daban da hannu biyu biyu, muna maraba da su shiga taron wasannin Olympic na Beijing da kallon gasanni. Jama'ar Sin za su maraba da bakinmu na kasashen duniya da hannu biyu biyu.'(Tasallah)