Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-02 21:37:02    
(Sabunta)An shirya liyafa a ofisoshin jakadanci na kasar Sin a kasashe daban daban don murnar ranar bikin kafa rundunar sojojin kwatar 'yancin jama'ar kasar Sin

cri

A ran 1 ga wata, an shirya liyafa a ofisoshin jakadancin Sin da ke kasashen Zimbabwe da Kamaru da Zambia da Jamus da kuma Finland, domin taya murnar ranar cika shekaru 80 da kafa rundunar sojojin kwatar 'yancin jama'ar kasar Sin.

A gun liyafar da aka yi, hafsan soja na ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Zimbabwe Tian Jianjun ya ba da jawabi cewa, inganta hadin kai da mu'amalar da ake yi tsakanin rundunar sojojin bangarori biyu ta kara dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu. Babban jami'in hukumar tsaron kasa ta kasar Zimbabwe da ya halarci wannan liyafa, ya nuna cewa, yana fatan abokantaka tsakanin kasashen biyu da rundunonin sojojin biyu za ta ci gaba har abada.

Ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke Kamaru da Zambia kuma sun kira liyafa domin taya murnar ranar cika shekaru 80 da kafa rundunar sojojin kwatar 'yancin jama'ar kasar Sin.(Danladi)