Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-02 19:55:34    
Sin za ta kara kayyade cinikin da take yi ta hanyar gyaran kayayyaki

cri
Kwanan baya, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin tare kuma da babbar hukumar kula da kwastan ta kasar sun fito fili da jerin sabbin sunayen kayayyakin da za a kayyade gyara su domin yin cinikinsu, inda aka kara sabbin kayayyakin da yawansu ya kai 1,800. A yayin da wata jami'ar ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ke hira da wakilinmu, ta ce, dalilin da ya sa aka habaka yawan kayayyakin da za a kayyade gyara su domin cinikinsu shi ne, don neman kyautata tsarin kayayyakin da Sin ke fitarwa zuwa kasashen waje, a sa kaimi ga kera kayayyaki masu daraja da kuma sassauta sabanin ciniki.

An ce, sabbin kayayyakin da aka kara sun hada da kayayyakin roba da kayayyakin alatu da na saka da kuma na karfe da sauransu. Sakamakon hakan, yawan kayayyakin da aka kayyade su ya karu har ya wuce 2,200 gaba daya. Nan gaba, masana'antun da ke gyaran kayayyakin da aka kayyade dole ne su biya kudin ba da tabbaci, wanda zai kara wa kamfanonin kudin gudanar da harkokinsu. A yayin da take tabo magana kan dalilin da ya sa aka gyara manufar, madam Wang Qinhua, shugabar sashen kula da masana'antun lantarki da na zamani da ke karkashin jagorancin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ta ce,"dalilin da ya sa muka kara kayyade wadannan sabbin kayayyaki shi ne don neman kyautata tsarin kayayyakin da muke fitarwa zuwa kasashen waje, mu sassauta sabanin ciniki da kuma sa kami ga masana'antun gyaran kayayyaki da su gyaru da kuma kara bunkasa. A shekarar da muke ciki, mai yiwuwa ne za mu gabatar da jerin kayayyakin daban da za a hana su ko kuma kayyade su."

Tun bayan da Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga kasashen waje, Sin tana ta kokarin bunkasa cinikin gyaran kayayyaki, har ma ta cimma gaggaruman nasarori a wannan fanni. Irin cinikin da aka yi ta hanyar gyaran kayayyaki ba ma kawai ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar ba, har ma ya kara samar da guraben aikin yi, ya tabbatar da kwanciyar hankalin al'umma ke nan.

Amma duk da haka, a yayin da cinikin gyaran kayayyaki ke sa kaimi ga cinikin da Sin ke yi da kasashen waje tare kuma da karuwar tattalin arzikin kasar, ya kuma kasance wasu matsalolin da dole ne a daidaita su a cikin irin cinikin da Sin ke yi ta hanyar gyaran kayayyaki. A halin yanzu dai, cinikin da Sin ke yi ta hanyar gyaran kayayyaki ba shi da inganci, kuma an fi mai da hankali kan harhada na'urori da kuma kera wasu kananan kayayyaki a lokacin da ake gyaran kayayyaki, sa'an nan aikin na bukatar dimbin leburori, ba a samu fasahohin zamani a cikin kayayyakin ba.

A cewar malama Wang Qinhua, shugabar sashen kula da masana'antun lantarki da na zamani na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, game da wadannan matsalolin da suka taso a fannin cinikin da aka yi ta hanyar gyaran kayayyaki, Sin ta tsai da kudurin kara kayayyade cinikin da aka yi ta hanyar gyaran kayayyaki masu araha. Wannan wani muhimmin matakin ne da Sin ta dauka ta fuskar tabbatar da manufarta ta samun dauwamammen cigaba, wanda zai taimaka wajen sassauta matsalolin karancin makamashi da gurbaccewar muhalli da ake fuskanta, haka kuma zai sai kaimi ga ingantuwar cinikin da aka yi ta hanyar gyaran kayayyaki da kuma tabbatar da bunkasuwar cinikin da Sin ta yi da kasashen waje cikin daidaici.

Madam Wang Qinhua ta kuma kara da cewa, ma'aikatar kasuwanci ta Sin za ta sa kaimi ga masana'antun da ke gyaran kayayyaki da su kaura zuwa shiyyoyi marasa cigaba da ke tsakiyar kasar Sin da kuma yammacinta, ta ce,"sabo da kudaden da ake bukata wajen gudanar da harkokin masana'antunn a tsakiya masu yammacin kasar Sin sun yi kasa idan an kwatanta da sauran yankuna, ga shi kuma an fi samun fifiko a fannin kwadago a shiyyar, cinikin gyaran kayayyaki zai kara samun cigaba a tsakiya maso yammacin kasar Sin, kuma tabbas ne za su sami maraba daga hukumar wurin da kuma masana'antunsa."(Lubabatu)