Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-01 18:37:12    
An yi babban taron murnar cikon shekaru 80 da kafuwar rundunar sojan 'yantar da jama'ar Sin a nan birnin Beijing

cri
Yau 1 ga wata da safe, a babban dakin taro na jama'ar kasar Sin da ke nan Beijing, an yi babban taron murnar cikon shekaru 80 da kafuwar rundunar sojan 'yantar da jama'a ta kasar Sin da kuma na wakilan jarumai sojoji da ke ba da misalai, inda shugaba Hu Jintao, da Wu Bangguo, da Wen Jiabao, da sauran kusoshin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar Sin suka halarta.

Babban sakataren kwamitin tsakiya na J.K.S, kuma shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin aikin soja ns tsakiya na kasar Sin Hu Jintao ya yi jawabi cewa, a cikin wadannan shekaru 80 da kafa rundunar sojan 'yantar da jama'ar Sin, rundunar sojan kasar Sin sun mai da hankulansu kan ba da hidima ga jama'ar Sin, kuma sun yi kokari wajen kiyaye 'yancin kan kasa da mutuncin al'umma, da bunkasuwar zaman takewar al'umma, kazalika sun ba da muhimman taimako a fannonin kiyaye zaman lafiya a duniya, da sa kaimi ga ci gaban 'dan Adam.

Shugaba Hu Jintao ya ce, a cikin shekarun nan 80, sojan 'yantar da jama'ar Sin sun nuna kyakkyawar al'adar juyin juya hali, a karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis, sun nuna bauta wa jama'a. Shugaba Hu ya bukaci duk sojan 'yantar da jama'ar Sin da su ci gaba da yada kyakkyawar al'adar gargajiyarsu, da tabbatar da madaidaicin nufin raya rundunar sojan, da kuma tabbatar da sauke nauyin da ke wuyansu kamar yadda ya kamata.

Shugaba Hu ya nuna cewa, a sabon lokacin tarihi, ya kamata a mai da ra'ayin raya kasa ta hanyar kimiyya da ya zama muhimmiyar manufar jagoranci wajen kara raya tsaron kasa da rundunar sojoji, da kuma sa kaimi ga zamanintar da harkokin tsaron kasa da rundunar sojoji. (Bilkisu)