Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-01 15:50:47    
Wani dan wasan tseren keke na kasar Sin na da burin shiga gasar tseren keke ta zagaya Faransa

cri
A kwanan baya, a birnin Xining da ke yammacin kasar Sin, an rufe gasar tseren keke kan hanyar mota da ke kewayen tabkin Qinghai a karo na 6, wanda aka yi kwanaki 10 ana yinta. A matsayin dan wasa na farko na kasar Sin da ya shiga tim din tseren keke mafi fice a duniya, malam Li Fuyu ya yi fintikau a gun gasar, ya kwashe lambar yabo ta dan wasa mafi nagarta a Asiya a cikin matakai 7 na farko a gun gasar. Amma duk da haka, Li Fuyu bai gamsu da halin da yake ciki a yanzu ba, domin yana da babban buri.

Li Fuyu ya shiga tim din tseren keke na Marco Polo na kasar Netherlands a shekarar 2005, ta haka ya shiga jeri na farko na kwararrun 'yan wasan tseren keke na kasar Sin. Ya shiga gasar taron wasannin motsa jiki ta Asiya a birnin Doha a shekarar 2006 a madadin kasar Sin. Saboda ya shiga shahararriyar tim din tseren keke na Discovery Channel na kasar Amurka a watan Janairu na shekarar 2007, ya zama dan wasa na farko a tarihin kasar Sin, wanda ya shiga tim mafi fice na kwararrun 'yan wasan tseren keke a duniya. A shekaru 3 da suka wuce, Li Fuyu ya sami kyakkyawan ci gaba 3 a jere. Mai jagorancin tim din tseren keke na Discovery Channel na Amurka ya nuna babban yabo ga mambarsa cewa, Li Fuyu, dan wasan tseren keke ne mafi kyau a Asiya.

Saboda nagartacciyar kwarewa da fasaha, Li Fuyu ya sami kujerarsa a rukunin kwararrun 'yan wasan tseren keke na duniya, inda gwanaye da yawa ke karawa da juna. A gun wasu muhimman gasannin tseren keke da aka yi a Asiya da Turai, Li Fuyu ya ci manyan nasarori, ya yi abin tarihi a kasar Sin.

Domin irin wadannan nasarori ne tim din na Discovery Channel na Amurka ya shigar da Li Fuyu a ciki. A gun gasar tseren keke kan hanyar mota da aka yi a kewayen tabkin Qinghai a wannan karo, Li Fuyu ya waiwayi abubuwan da suka wakana a da, ya ce,'Saboda na ci wasu gasanni, haka kuma, watakila tim din ya yi shirin shigar da 'yan wasan Asiya a ciki. Na ci wasu gasannin da aka yi a Turai, shi ya sa shugabannin tim din suke kaunata.'

Tim din tseren keke na Discovery Channel na Amurka na daya daga cikin tim-tim na kwararrun 'yan wasan tseren keke guda 20 mafiya fice a duniya. A cikin wannan tim da ke kan gaba a duniya, Li Fuyu ya bude kansa wani sabon shafi. Ba kawai ya kara samun damar shiga gasanni da yawa ba, har ma ya kara fahimtar hanyoyin da kwararru suke bi a fannonin tafiyar da tim da horar da 'yan wasa da kuma yin gasa. A rabin shekara da ya gabata, kwarewarsa ta yin takara ta sami kyautatuwa sosai. Li Fuyu ya ce,'Ina tsammani cewa, kwarewata ta sami kyautatuwa kadan bisa ta shekarar bara, na fi samun ci gaba a fannin taimakawar abokaina na tim din ta fuskar fasaha da kuma dabarar yin gasa, ban da wannan kuma, na kara fahimtar sauran abubuwa.'

Saboda Li Fuyu ya shiga tim din da mashahurin dan wasa Lance Armstrong na Amurka ya taba aiki a ciki, shi ya sa an kusantar da 'yan wasan tseren keke na kasar Sin da gasar tseren keke ta zagaya Faransa. Li Fuyu yana alla-alla wajen shiga gasar tseren keke ta zagaya Faransa, wadda ke kan matsayin koli a fannin wasan tseren keke. A idonsa, shiga wannan muhimmiyar gasa burinsa ne.

Kasar Sin tana kan gaba wajen yin amfani da kekuna, amma tana bukatar yin ayyuka da yawa domin zama kasa mai karfi a fannin wasan tseren keke. Bullowar Li Fuyu sau da yawa a gun gasannin kasa da kasa ta zabura wajen bunkasuwar wasan tseren keke na kasar Sin, haka kuma, ta sa kaimi ga 'yan wasan kasar Sin masu yawa da su shiga tim-tim na kwararrun 'yan wasan tseren keke na duniya sosai. Don zama kan gaba a fannin wasan tseren keke a duniya, yanzu daga karfin dukkan 'yan wasanta cikin sauri ya fi muhimmanci ga kasar Sin. Li Fuyu ya ba da shawara kan yadda 'yan wasan Sin suka kawar da cikas wajen kyautata kwarewar kansu, ya ce,'Ina ganin cewa, ya zama wajibi ne su shiga wasu manyan gasanni na duniya cikin himma da kwazo, sannu a hankali za mu saje da gasanni iri daban daban.'

A watan Yuni na shekarar da muke ciki, Li Fuyu ya hada kansa da abokansa na tim din Discovery Channel na Amurka wajen zama na 4 a gun gasar tseren keke da aka yi cikin kungiya-kungiya tare da kidayar lokaci a Netherlands, wadda wani bangare ne na gasar tseren keke da hadaddiyar kungiyar tseren keke ta kasa da kasa wato UCI ta yi a kasashe da yawa, sa'an nan kuma, ya sami damar shiga gasannin wasannin Olympic na Beijing. Li Fuyu yana sa ran alheri domin shiga gasannin wasannin Olympic da za a yi a kasar mahaifiyarsa, yana kuma fatan samun maki mai kyau a gun gasannin, ta haka ba zai kauce wa kyakkyawan fatan alheri da Sinawa suke nuna masa ba.(Tasallah)