Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-01 15:50:47    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(26/07-01/08)

cri
Da farko, ga wani labari game da taron wasannin Olympic da za a yi a nan Beijing a shekara mai zuwa. Ran 28 ga watan Yuli, an kammala gina wurin yawon shakatawa na ruwa na Olympic na Shunyi da ke Beijing da kuma dakin wasan harbe-harbe na Beijing a hukunce. Wadannan filayen wasa 2 sun kasance a matsayin sabbin filaye da dakunan wasa na rukuni na farko da za a kaddamar da yin amfani da su domin taron wasannin Olympic na Beijing.

Ran 29 ga watan Yuli, a birnin Amman, hedkwatar kasar Jordan, an rufe gasar fid da gwani ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta Asiya a karo na 17 mai tsawon kwanaki 5. Kungiyar kasar Sin ta sami lambobin zinariya 7 da na azurfa 5 da kuma na tagulla 4 a cikin dukkan kananan gasanni 44, ta haka ta zama ta farko a cikin dukkan jerin kasashen Asiya wajen samun lambobin zinariya da kuma samun lambobin yabo. Kungiyar kasar Indiya ta zama ta biyu saboda samun lambobin zinariya 5. Za a yi gasar fid da gwani ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta Asiya a karo na 18 a birnin Guangzhou na kasar Sin a shekarar 2009.

A watan Satumba, a nan kasar Sin, za a yi zagaye na karshe ta gasar cin kofin duniya na wasan kwallon kafa ta mata ta shekarar 2007. Ran 23 ga watan Yuli, an kaddamar da sayar da tikitin shiga gasanni a biranen da za su shirya gasannin.

Ran 29 ga watan Yuli, a birnin Jakarta, hedkwatar kasar Indonesia, an rufe gasar cin kofin Asiya ta wasan kwallon kafa a karo na 14. A cikin karon karshe da kungiyoyin kasashen Iraq da Saudi Arabia suka yi, dan wasa Younis Mahmoud na Iraq ya jefa kwallo guda zuwa ragar kungiyar kasar Saudi Arabia a minti 71 na gasar, shi ya sa kungiyar Iraq ta lashe kungiyar Saudi Arabia, ta zama zakara a karo na farko a tarihinta. A gun gasar neman zama ta uku da aka yi ran 28 ga wata, kungiyar kasar Korea ta Kudu ta lashe kungiyar kasar Japan da cin 6 da 5 a cikin buga kwallo daga kai sai mai tsaron gida, ta haka ta zama ta uku a gun gasar.

Ban da wannan kuma, a wannan rana, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta Asiya ta sanar da cewa, kasar Qatar za ta shirya gasar cin kofin Asiya ta wasan kwallon kafa a shekarar 2011, amma duk da haka, za ta shirya gasar a watan Janairu saboda zafi mai tsanani a wurin.(Tasallah)