Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-01 15:40:15    
Bukin nune nunen kayan soja da aka gudanar a Beijing ya kasance wani kasaitaccen lamari

cri
Bukin nune nunen kayan soja da aka gudanar a Beijing, inda aka nuna irin ci gaban da aka samu a rundunar sojan 'yantar da jama'a ta kasar Sin (PLA) cikin shekaru tamanin da suka gabata, ya kasance wani kasaitaccen lamari a birnin Beijing, abin da ya janyo ra'ayin miliyoyin jama'a suka zo kallon irin makaman zamani da kayan aikin soja na zamani da rundunar sojan take da su.

Daga cikin bakin da suka je kallon wannan bukin nune nunen kayan soja, baya ga jami'an gwamnati da jami'an soja da sauran jama'ar gari, har ma akwai tsaffin shugabanni da manyan jami'an soja da suka yi ritaya.

Tsohon shugaban Sin, Mr. Jiang Zemin, shi ma ba a bar shi a baya ba, wajen halartar wannan buki nune nunen kayan soja, da aka gudanar jiya Talata da dare, ya kuma nuna sha'awarsa kan nune-nunen, da kuma irin ci gaban da rundunar sojan ta samu cikin shekaru tamanin da suka gabata.

Mr, Jiang, wanda kuma ya taba rike mukamin shugaban hukumar soja ta tsakiya, cewa ya yi, wannan bukin nune nunen kayan sojan, zai kasance tamkar wani littafi ne dake bayyana irin jan hali na juyin juya halin rundunar sojan ta kasar Sin. Yayin da yake sauraren bayanin da wani jami'i ke yi kan kayan aikin na soja, Mr. Jiang ya kan dakatar da jami'in, domin neman karin bayani dangane da wani irin makamin da bai fahimci yadda ake amfani da shi ba.

Mr Jiang ya kara da cewa bukin nunin ya bayyana cewa rundunar sojan PLA dake karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Sin, wata rundunar soja ce ta jama'a, kuma ginshikin kasa, sannan kuma ta bayar da gagarumar gudummuwa a juyin juya halin kasar, da sake gina kasa da aiwatar da sauye sauye. Don haka ya kamata mu yi biyayya ga shugabancin Hu Jiantao a matsayin babban sakatare, domin bunkasa rundunar sojan ta kasance ta zamani ta yadda sha'anin tsaron kasa zai inganta. [Lawal]