Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-01 10:40:49    
Labari mai dumi dumi: An yi babban taron murnar cikon shekaru 80 da kafuwa rundunar sojan 'yantar da jama'ar Sin a Beijing

cri
Ran 1 ga watan Agusta da safe, a babban dakin taro na jama'ar kasar Sin da ke nan Beijing, an yi babban taron murnar cikon shekaru 80 da kafuwar rundunar sojan 'yantar da jama'a ta kasar Sin da kuma na wakilan jarumai sojoji da ke ba da misalai, inda malam Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da sauran kusoshin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar Sin suka halarci taron. Firayim minista Wen Jiabao ya shugabanci taron. Babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin tsakiya na rundunar sojan kasar Sin Mr. Hu Jintao ya ba da muhimmin jawabi a gun taron.

Ran 1 ga watan Agusta na shekarar 1927, Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta jagoranci boren da aka yi a birnin Nanchang na lardin Jiangxi da ke kudu maso tsakiyar kasar Sin, ta haka, rundunar soja ta juyin juya hali da ke karkashin shugabancin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta kafu.(Tasallah)