Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-31 21:12:00    
Ma'aikatar tsaron kasa ta Sin ta shirya liyafa don murnar ranar cika shekaru 80 da kafa rundunar sojojin kasar

cri

Ran 31 ga wata da dare, a nan birnin Beijing, ma'aikatar tsaron kasa ta Sin ta shirya liyafa don munar ranar cika shekaru 80 da kafa rundunar sojojin kwatar 'yancin jama'ar kasar Sin. A cikin jawabin da ya yi a gun liyafar, Cao Gangchuan, ministan tsaron kasar ya bayyana cewa, rundunar sojojin kwatar 'yancin jama'ar kasar Sin tana so ta kara yin musanya da hadin kai a tsakaninta da rundunonin sojoji na kasashe daban daban, don ba da sabon taimako wajen kiyaye zaman lafiya a duniya.

Mr Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da sauran shugabannin jam'iyyar Kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar sun halarci liyafar.

A cikin jawabinsa, Cao Gangchuan ya waiwaye tarihi mai haske da nasarori da rundunar sojojin kasar Sin ta samu a cikin shekaru 80 da suka wuce. Ya kara da cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen raya kasa ta hanyar zaman lafiya, ko da yaushe tana aiwatar da manufar zaman lafiya game da harkokin waje cikin rike mulkin kai ba tare da tsangwama ba, da manufar tsaron kasa don tsaron kai, tana kokari sosai wajen hadin kanta da jama'ar kasashe daban daban, don sa kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa, da samun wadatuwa tare da zaman jituwa a duniya.

Bayan haka Cao Gangchuan ya jaddada cewa, rundunar sojojin kasar Sin za ta ci gaba da nuna sahihanci sosai, ta yi iyakacin kokari wajen sa kaimi ga yalwata hulda a tsakanin bangarori biyu na mashigin teku na Taiwan cikin lumana, don neman dinkuwar kasa cikin lumana, amma ko kusa, ba za ta yi hakuri da 'yancin kan Taiwan ba, kuma ko kusa ba ta yarda da wanda ya balle Taiwan daga kasar Sin ta ko wace hanya ba. Rundunar sojojin kasar Sin ta dau niyya, ta kasance cikin shiri, kuma tana da karfi wajen hana 'yancin kan Taiwan da aukuwar duk wani babban al'amari da zai haifar da 'yancin kan Taiwan, kuma ta tsaya tsayin daka wajen kare mallakar kan kasar Sin da cikakken yankin kasar. (Halilu)