Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-31 15:32:58    
Cin cakulan na madara ya amfana wa kara kwarewar tunani

cri

Bisa labarin da kafofin yada labaru na kasar Amurka suka bayar a kwanan baya, an ce, bincike mai dumi dumi da masu ilmin kimiyya na kasar Amurka suka yi ya nuna cewa, cin cakulan na madara yana amfana wa kara wa mutane kwarewar tunani.

Masu bincike na kasar Amurka sun raba mutane cikin rukunoni 4, daga baya kuma, mutanen rukuni na farko sun ci cakulan na madara gram 85, mutane na rukuni na 2 sun ci bakin cakulan gram 85, mutane na rukuni na 3 sun ci garin waken carob da a kan ci shi a maimakon cakulan gram 85, mutane na rukuni na 4 ba su ci kome ba. Bayan mintoci 15, an yi musu bincike ta fuskar kwakwalwa da halin dan Adam bi da bi, don yin bincike kan kwarewar tunani da kulawa da lokacin daukar matakai da kuma kwarewar warware matsaloli.

Sakamakon da aka samu ya shaida cewa, mutanen da suka ci cakulan na madara sun fi rike da abubuwa a cikin zukatansu ta hanyoyin karanta da idanu, in an kwatanta su da sauran mutanen da aka yi bincike kansu, wadanda suka ci cakulan nan madara da bakin cakulan sun karfafa kwantar da zuciya da kuma lokacin daukar matakai.

Mai kula da wannan bincike ya bayyana cewa, cakulan yana kunshe da theobromine da caffeine da sauran abubuwan da ke sa kaimi kan kwakwalwar mutane. A da mutane suna ganin cewa, wadannan abubuwan sun ba da taimako ga mutane wajen lura da kuma mai da hankali kan abubuwa, amma sakamakon da suka samu ya nuna cewa, bayan da wani mutum ya ci cakulan, ya yi zumudi, ta yadda za a karfafa hazakarsa.

Binciken da aka yi a da ya nuna cewa, wasa abubuwa masu gina jiki da ke cikin abinci suna amfana wa rabuwar sukarin inabi da kuma sa kaimi kan bugun jini, ta yadda za a kara wa mutane kwarewar fahimi.(Tasallah)