Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-31 13:59:12    
Kasar Sin za ta halarci aikin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. cikin himma

cri
A ran 31 ga wata, bisa labarin da aka buga a cikin shafin labarun waje na jaridar People Daily, an ce, Kasar Sin za ta halarci ayyukan kiyaye zaman lafiya na M.D.D. cikin himma, domin tabbatar da kishinta kan zaman lafiya, haka kuma ta shiga harkokin M.D.D. cikin himma domin sauke nauyin dake bisa wuyan babbar kasa ta Sin. Yanzu, Kasar Sin ta jibge rundunoni guda 10 dake kunshe da sojoji 1546, a yankunan aiki guda 4 na M.D.D. Kasar Sin tana daya daga cikin kasashen da suke tura rundunonin sojoji mafi yawa daga cikin zaunannun kasashe na kwamitin sulhu na M.D.D.

Kididdiga ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu, Kasar Sin ta riga ta halarci ayyukan kiyaye zaman lafiya guda 17 na M.D.D. Yawan sojojin da ta tura ya kai 7511, hafsoshi 3 da sojoji 5 sun mutu lokacin da suka yi aikin kiyaye zaman lafiya.

Tun da Kasar Sin ta halarci aikin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. Tsawon hanyoyin da rundunonin sojanta suka gina ko kuma suka gyara ya kai kilomita dubu 10 ko fiye, yawan gadojin da suka gina ya kai 207,kuma sun kau da boma-bomai 7500 ko fiye. Rundunonin sufuri sun yi sufurin kayan ton dubu 210, tsawon hanyoyin da suka bi ya kai kilomita miliyan 3.5. Mutane marasa lafiya da likitocin soja na Kasar Sin suka warkar da su sun kai wajen dubu 30. (Asabe)