Lokacin da ake murnar cikon shekaru 80 da kafuwar rundunar soja ta 'yantar da jama'ar Sin, wani babban hafsan ma'aikatar samar da na'urorin soja ta rundunar ya gaya wa manema labaru cewa, a matsayin tushen fasahohi da kayayyaki na kokarin zamanintar da rundunar soja ta tsaron kasar ne, aka riga aka kafa tsarin samar da makamai da na'urorin soja na zamani na wucin gadi a cikin rundunar sojan 'yantar da jama'ar Sin.
Wannan babban hafsa ya ce, bayan da aka yi kokari ba tare da tangarda ba a cikin shekeru masu yawa da suka wuce, tsarin makamai da na'urorin soja na rundunar soja ta 'yantar da jama'ar Sin ya yi ta samun kyautatuwa. A bayyane ne an kara karfin yin yaki da karfin kare kai na rundunar soja ta 'yantar da jama'ar Sin. Sabo da haka, tana tsaron ikon mulkin kasar da cikakkun yankunan kasar da kwanciyar hankali na Sin.(Sanusi Chen)
|