Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-30 11:50:30    
Hafsoshi da sojoji 1600 na kasar Sin za su shiga rawar daji ta "shirin zaman lafiya ta 2007" domin yaki da ta'addanci

cri
A ran 9 ga watan Agusta a cikin hadin guiwa ne za a soma rawar daji ta "shirin zaman lafiya ta 2007". Hafsoshi da sojoji 1600 na kasar Sin za su shiga wannan rawar daji.

Yanzu, sojoji da na'urorin soja da aka yi jigilarsu ta hanyar dogo sun riga sun isa kasar Rasha, rukunonin jiragen sama masu saukar ungulu na kasar Sin da za su halarci wannan rawar daji sun kuma soma canja filayen saukar jiragen sama.

A ran 30 ga wata, kanar Lu Chuangang, shugaban rukunin ba da umurni na sashen shirya wannan rawar daji na bangaren kasar Sin ya gawa wa kafofin watsa labaru cewa, yaya za a yi yaki da barazanar da ba a saba samun irinta ba, wani sabon batu ne da ke gabanmu. Wannan rawar daji da za a yi wata dama ce wajen kokarin neman jerin tunanin yin yaki da ta'addanci, kuma za a yi wadannan sabbin tunani cikin hakikanan matakan yaki da ta'addanci da kasashe 6 na kungiyar hada kai ta Shanghai za su dauka cikin hadin guiwa. (Sanusi Chen)