Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-30 16:14:38    
Kasar Sin ta kaddamar da shirin bunkasa muhimman kimiyya da fasahohi

cri

Ba da jimawa ba ne, kasar Sin ta kaddamar da wani sabon shiri kan bunkasa muhimman kimiyya da fasahohi domin kara karfin kimiyya da fasaha wajen nuna goyon baya ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar daga dukkan fannoni. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wannan batu.

An kaddamar da wannan shiri ne a watan Fabrairu na shekarar da muke ciki, kuma an kiyasta cewa, za a zuba kudaden Sin wato Yuan biliyan 30 a cikin shirin. Gwamnatin kasar Sin ta yi fatan cewa, ta hanyar aiwatar da shirin, za a iya sassauta matsalolin makamashi da albarkatu da muhallin halittu da ke yin illa ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar a cikin shekaru da dama masu zuwa, ta yadda za a iya daga matsayin kimiyya da fasaha a fannin ba da hidima ga jama'a. Game da shirin, wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin Madam Chen Zhili ta nuna cewa,

"An tsara da kuma aiwatar da shirin bunkasa muhimman kimiyya da fasahohi na kasa ne domin ba da taimako ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Sin kai tsaye. Ta shirin, kasar Sin za ta yi kokari wajen warware wasu matsalolin muhimman fasahohi na jin dadin jama'a da na sana'o'i, da samun manyan sakamako masu kyau da ke da ikon mallakar ilmi mai cin gashin kai, da kuma horar da wasu kamfanonin da ke da karfin takawa a duk duniya, ta yadda za a iya warware matsalolin da ke kawo cikas ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Sin."

A da, kasar Sin ta taba aiwatar da wani shiri kamar haka, wanda ake kiransa "shirin warware matsalolin kimiyya da fasaha na kasar Sin". Bisa labarin da muka samu, an ce, bayan da aka fara aiwatar da shirin warware matsalolin kimiyya da fasaha a shekaru 80 na karnin da ya gabata, kasar Sin ta yi nazari da kuma samun wasu muhimman fasahohi, kamar shuka shimkafa mai aure, da muhimmin aikin ruwa na dam din Sanxia da aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta yin amfani da karfin nukiliya ta Qinshan da dai sauransu, ta haka an samu babbar moriya a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma.

Yanzu kasar Sin ta riga ta taka wani sabon mataki wajen samun bunkasuwa, kuma tana fuskantar kalubale mai tsanani a fannonin makamashi da albarkatu da muhallin halittu da shawo kan manyan cututtuka da kara karfin takara na sana'o'i da tsaron kai na jama'a. Shi ya sa tsohon shirin ya kasa biyan bukatun kasar Sin na yanzu.

Sabo da haka, bisa tushen shirin warware matsalolin kimiyya da fasaha, kasar Sin ta tsara shirin bunkasa muhimman kimiyya da fasahohi domin tattara albarkatun kimiyya da fasaha masu rinjaye na duk fadin kasar wajen nuna goyon baya ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta. Shugaban sashen tsara shirin bunkasuwa na ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin Wang Xiaofang ya bayyana cewa, shirin ya shafi fannoni 11 kamar aikin gona da kayayyaki da kuma sana'ar hada-hada da dai sauransu, kuma zai nuna goyon baya ga ayyuka kusan 350. Yanzu an riga an tabbatar da ayyuka na rukunin farko da za a tallafa musu. Kuma ya kara da cewa,

"da farko, shirin ya kebe kudade Yuan biliyan 7.35 domin tallafa wa ayyuka 147. Kuma ana sa ran cewa, wadannan kudaden da gwamnatin kasar Sin ta zuba za su kara kwarin gwiwar masana'antu da sauran bangarorin da abin ya shafa wajen kara kudaden da za su kebe, kuma yawan kudaden zai ninka a kalla sau biyu bisa na lokacin da."

Kamfanin fasahar zamani na Tian Huihua na kasar Sin yana yin nazari kan wata na'urar zamani domin gano cuta a jikin mutum da ake kiranta B ultrasound a bakin turawa, kuma an shiga da aikin a cikin ayyuka na rukunin farko da shirin bunkasa kimiyya da fasaha zai tallafa musu. Shugaban kamfanin Shen Jianlei ya gaya wa wakilinmu cewa,

"shirin ya samar da kudade Yuan miliyan uku, kuma kamfanninmu ya samar da kudade Yuan miliyan uku, ta haka mun jawo hankulan zaman al'umma sosai, kuma yawan kudaden da muka samu daga zaman al'umma zai kai Yuan miliyan 60, shi ya sa shirin ya taka muhimmiya rawa."

Ban da wannan kuma wakilinmu ya gano cewa, mutanen da ke sashen kimiyya da fasaha na kasar Sin suna ganin cewa, tare da aiwatarwar shirin bunkasa muhimman kimiyya da fasahohi na kasa, dole ne za a iya kara karfin kimiyya da fasaha wajen goyon bayan bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin.(Kande Gao)