Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-30 15:09:46    
Dakarun sojan kasar Sin sun kammala wani shirin horo na hadin guiwa na farko tare da dakarun kasar Thailand

cri

Jiya lahadi ne wani rukunin dakarun soja na musammam, na rundunar sojan 'yan tar da jama'a ta kasar Sin suka kammala wani kwas din horaswa na kwanaki 13, tare da takwarorinsu na rundunar sojan kasar Thailand, a makaranta horon soja ta kasar Sin dake garin Guangzhou.

Wannan kwas din horaswa da aka yi wa lakabi da "shock Action 2007" shi ne karo na farko da sojojin rundunar sojan 'yantar da jama'a ta kasar sin ta gudanar da horon hadin guiwa, tare da sojojin kasashen waje. A cewar wani jami'i a ma'aikatar tsaro ta kasar Sin, Jia Xiaoning, kwamandojin sojan Sin da na Thailand ne suka hada karfi wajen bayar da horon.

Jiya lahadi ne wadannan dakarun soja na musammam, suka kammala wannan kwas tare da darasi na karshe, a kan ceto wadanda akayi garkuwa da su, da kuma fatattakar kungiyar masu hada hada da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

A cewar Jia, yayin gudanar da wannan kwas da aka kwashe tsawon kwanaki 13 ana yinsa, jami'ai da dakarun soja na kasashen biyu, wato Sin da Thailand sun samu horo kan yaki a kasa, jimre rayuwa cikin kungurmin daji, dubarun shiga cikin ruwa, da sauran dubarun yaki. [Lawal]