Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-27 16:56:12    
Ana himmantuwa wajen share fage ga gudanar da gasar sukuwar dawaki ta taron wasannin Olympic a yankin Hongkong

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, a cikin birane guda shida masu bada taimako ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing, akwai wani birni dake da tazarar kusan kilo-mita 3,000 daga nan Beijing, shi ne yankin Hongkong, inda za a gudanar da gasar sukuwar dawaki ta taron wasannin Olympic. Kwanakin baya ba da dadewa ba,, wakilinmu ya kai ziyara a filin wasan sukuwar dawaki da ake kusan kammala gina shi a yankin Hong Kong.

Wata malama mai aikin sa kai ta wasan sukuwar dawaki na taron wasannin Olympic na Beijing ta dau alkawari ga aminai daga duk fadin duniya cewa " Hong Kong wani karamin birni ne. Amma za mu iya sanya kokari matuka wajen gudanar da gasar".

A cikin tarihin taron wasannin Olympic, filin yin gasar wasa daya tilo na da tazarar kilo-mita sama da 1,000 daga birni mai masaukin taron wasannin. Lallai sau daya ne kawai aka taba ganin kamar irinsa, wato ke nan a gun taron wasannin Olympic na Melbourne da aka gudanar a zamanin shekarar 1950 na karnin da ya gabata, saboda dakilin dudduba ingancin dabbobi ne, aka yanke shawarar gudanar da gasar sukuwar dawaki a kasar Sweden. Saboda irin wannan dalili ne kuwa, a watan Yuli na shekarar 2005, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya tsaida kudurin mayar da yankin Hong Kong a matsayin wurin gudanar da gasar sukuwar dawaki ta taron wasannin Olympic na Beijing. Ko da yake yankin Hongkong yana da kyakkyawar al'ada wajen gudanar da gasar sukuwar dawaki da kuma dimbin kwararru na sana'ar musamman, wadanda suka shiga ayyukan share fage ga gudanar da gasar sukuwar dawaki, amma yana fuskantar wani babban kalubale wajen kammala wannan aiki cikin shekaru 3 da 'yan watanni kawai.


1 2 3