Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-27 12:36:34    
Rasha ta kara rike matsayinta kan "Yarjejeniyar makaman yau da kullum ta Turai"

cri
A ran 25 ga wata, Mr. Putin, shugaban kasar Rasha ya ce, a wancan zamani wato a lokacin da aka kulla "yarjejeniyar makaman yau da kullum ta Turai", ya kasance da manyan rukunonin soja guda 2 wato kungiyar tsaro ta Nato da kawancen Warsaw, amma yanzu wannan yarjejeniya ta riga ta wuce lokacinta. Wannan karo na 2 ke nan da Mr. Putin ya fito fili cikin wata daya don ba da ra'ayinsa kan "yarjejeniyar makaman yau da kullum ta Turai, wannan kuma ya bayyana cewa Rasha ta kara tsayawa kan matsayin da ta daukan kan Amurka da kungiyar tsaro ta Nato kan wannan matsala.

Yayin da Mr. Putin yake ganawa da manyan hafsoshin soja na hukumomi masu karfi na Rasha a wannan rana ya bayyana cewa, kusan a ce yanzu dukkan kasashen gabashin Turai sun riga sun shiga cikin kungiyar tsaro ta Nato, wato halin da ake ciki ya sauya da gaske, sabo da haka wannan yarjejeniya ta riga ta wuce lokacinta, kasar Rasha ta ga tilas ne ta dakatar da shirinta na gudanar da "yarjejeniyar makaman yau da kullum ta Turai" da sauran wasu yarjeniyoyin da abin ya shafa na kasashen duniya.

Wadannan maganganun da Mr. Putin ya yi a baya sun kalubalanci "yarjejeniyar makaman yau da kullum ta Turai" kan wajibcinta da gaskiyarta, kafin wannan wato a ran 14 ga wata kuma Mr. Putin ya riga ya rattaba hannu kan kudurin dakatar da shirin gudanar da "yarjejeniyar makaman yau da kullum ta Turai" da sauran wasu yarjeniyoyin da abin ya shafa na kasashen duniya.

Dalilin da ya sa kasar Rasha ta kara rike matsayinta kan "yarjejeniyar makaman yau da kullum ta Turai" shi ne, sabo da bisa wucewar lokaci halin da ake ciki ya sauya, kuma an gamu wasu matsaloli wajen gudanar da wannan yarjejeniya, ban da wannan kuma tsarin kakkabo makamai masu linzami da Amurke ta kafa a gabashin Turai shi ma ya zama wani muhimmin dalili. Wannan kuma ta shafi matsalar tsaron kasa da babbar moriya ta Rasha, a hakika kuwa Rasha ba za ta zuba ido tana kallo kawai ba.

Wani dalili daban da ya sa Rasha ta kara rike matsayinta kan "yarjejeniyar makaman yau da kullum ta Turai" shi ne, sabo da Amurka ba ta mai da martani ga shawarar da Mr. Putin ya bayar kan matsalar tsarin kakkabo makamai masu linzami ba. Bisa shawarar da Mr. Putin ya bayar an ce, za a iya yawaita yawan mambobi masu yin shawarwarin da ake yi tsakanin Rasha da Amurka kan matsalar tsarin kakkabo makamai masu linzami har zuwa sauran kasashen Turai da suke nuna sha'awa kan wannan matsala, amma da akwai wani sharadin farko wato shi ne, Amurka ba za ta kafa tsarin kakkabo makamai masu linzami a kasashen Cheks da Poland ba. Ko da yake Mr. Bush, shugaban kasar Amurka bai musunta shawarar da Mr. Putin ya gabatar kai tsaye ba, amma ya nanata cewa, "ya kamata Cheks da Poland su zama wani kashin da ba za a iya balle shi daga tsarin kakkabo makamai masu linzami ba." Bisa wannan hali, dole ne Rasha ta mai da martani mai tsanani, ta yadda za ta hana halin rashin daidaito tsakanin Rasha da Amurka a fannin muhimman tsare- tsare.

Manazarta sun bayyana cewa, da akwai wasu muhimman dalilan da suka sa kasar Rasha ta kara rike matsayinta kan "yarjejeniyar makaman yau da kullum na Turai" wato su ne, na farko, kungiyar tsaro ta Nato wadda Amurka ke shugabanta ta yi ta habaka karfinta zuwa yankin gabas. Na 2, Rasha ta yi haka ne don yin shirin janye jikinta daga "yarjejeniyar makaman yau da kullum na Turai". Na 3, halin da ake ciki yanzu cikin kasar Rasha ya samu kyautatuwa wajen siyasa da tattalin arziki, Mr. Putin kuma yana ta kara samun kwar jini a cikin kasar, wannan ya kara samar da karfin zuciya ga Rasha don ta yi gaba da Amurka da Turai.

Manazarta kuma sun bayyana cewa, ko Rasha ta janye jikinta daga "yarjejeniyar makaman yau da kullum ta Turai", ko kuma ta dakatar da shirinta don gudanar da yarjejeniyar, duk abin da za ta yi zai jawo tasiri ga halin da ake cikin wajen tsaron Turai. (Umaru)