Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-25 15:42:04    
Mai yin gadon fasahar gargajiya ta kasar Sin

cri

Bisa albarkacin bunkasuwar birane a kasar Sin, a kai a kai ne aka rasa sha'awar kaunar fasahohin gargajiya. Wakokin da aka rera tare da buga ganguna a birnin Wuning na lardin Jiangxi da ke da tarihi mai shekaru fiye da 200 su ma suna cikin fasahohin gargajiyar da aka rasa sha'awar kaunarsu. Yau za mu gabatar da wata mai fasaha da ke yunkurin kiyaye fasahar gargajiya da yin gadonta ta hanyar rera wakoki tare da buga ganguna wadda ake kiran ta da cewar wai: "Yar manyan tsaunuka", sunanta shi ne Chen Qin.

Idan manoman da ke zama a shiyyar tsaunuka ta gundumar Wuning suna aiki a gonaki, in mutane da yawa suke aiki tare da nuna faranta rai sosai, sai suke soma rera wakoki tare da buga ganguna don tayar da himmar aiki, wani lokaci , wani mutum ya buga ganga, sai mutane da yawa suke rera wakoki tare da amon gangar. Yanzu wakokin da aka rera tare da amon ganguna a gundumar Wuning ta lardin Jiangxi an riga an mayar da su a cikin sunayen abubuwan tarihi na al'adu ba kayayyaki ba bisa matsayin lardin.

Malama Chen Qin mai shekaru 38 ta yi girma a gundumar Wuning ta lardin Jiangxi. Tun lokacin da take karama, tana girma ne tare da saurarar wakokin da aka rera tare da amon ganguna da kuma kallon wasannin kwaikwayo irin na cire ganyayen shayi, Malama Chen Qin ta bayyana cewa, a wancan zamani, ba a sami akwaitin rediyo mai hoto a kauyuka ba, hakan kuma ba a nuna sinima da yawa ba, saboda haka rera wakoki tare da amon ganguna shi ne abin faranta rai gare mu, in mutanen iyalin suna rera wakoki, to suka yi farin ciki sosai fiye da halin da suke ciki na murnar sabuwar shekara.

Kakan Chen Qin shi ne mai kera ganguna da ya yi suna sosai, tun da malama Chen Qin take karama, ana kan gayyaci kakanta don rera wakoki tare da buga ganguna. A kwana a tashi, Malama Chen Qin ita ma ta soma sha'awar fasahar irin ta kauyuka. A shekarar 1984, malama Chen Qin ta shiga cikin ajin horar da 'yan wasan cire ganyayen shayi na makarantar koyar da fasahohi na lardin Jiangxi, bayan da ta sauka daga karatu, sai ta shiga cikin kungiyar nuna wasannin cire ganyaye shayi ta gundumar Wuning, tana kaunar aikinta sosai, amma a shekarar 1993, an yi watsi da kungiyarta, Malama Chen Qin ta yi bakin ciki sosai.

A shekarar 1995, ta fita waje ta yi ayyuka iri iri da yawa, amma kodayake ta zuwa wurare da yawa, amma ba ta manta da wakokin da aka rera a garinta ba. Ta bayyana cewa, a wancan lokaci, ina zama a birane, ga manyan gine-gine tare da fitilu masu haske tare da launuka iri iri a ko'ina, amma ga ni mutumiya ce da ke fitowa daga manyan tsaunuka, ban iya jan numfashi tare da shan iskar manyan tsaunuka ba, kuma ban iya saurarar kukan tsuntsaye tare da muryar malalar ruwa ba. Kai, zaman rayuwar da nake yi tamkar ba nawa ba ne.

Wata rana, Malama Chen Qin ta yi aiki tare da wasu aminan kasashen waje, an gayyace ta don rera wata waka, ashe! Wakar da ta rera tamkar yadda muryar da ta sauko daga sararin samaniya. Kowa ya yi mamaki da nuna sha'awa sosai da sosai.

Malama Chen Qin ita ma ta burge sosai, saboda haka ta tsai da kudurin koma gidanta.

Shigarta a garinta ke da wuya, sai ta ji ta sake shiga mafarkinta na lokacin yarantakarta.

Daga nan sai malama Chen Qin ta fita waje tare da guzurinta da inji mai dukar hoto da sauran abubuwa, ta suka ko'ina a gundumar Wuning don gana da tsofaffin masu fasahohi na wurin da kuma tattara wakokin da mutanen garinta suka rera tare da amon ganguna.

Ta ce, na riga na tattara wakoki da yawa da aka rera tare da amon ganguna wadanda yawansu ya kai dubu 20. A shekarar 2005, Malama Chen Qin ta buga wani littafin da ke da babban batu cewa, kauyuka da ke kan manyan tsaunuka da gangunan da aka buga tare da wakokin da aka rera a manyan tsaunuka, wato labari dangane da kaka. Littafin ya sami yabo daga wajen rukunin masu fasahohin al'adu na kasar Sin sosai. (Halima)