Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-25 08:27:29    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (18/07-24/07)

cri

Ran 17 ga wata,babban jami`in kwamitin wasannin Olimpic na duniya Urs Lacotte ya darajanta aikin share fage da kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na birnin Beijing yake yi domin taron wasannin Olimpic na shekarar 2008,Mr.Lacotte ya bayyana cewa,ko shakka babu birnin Beijing zai shirya mana wani taron wasannin Olimpic mai faranta ran mutanen duniya,ya ci gaba da cewa,kwamitin wasannin Olimpic na duniya ya gamsu da aikin share fage na kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing sosai da sosai,kawo yanzu,dukkan labaran da suka samu su ne labaru masu kyau,kuma ana gudanar da dukkan fannoni kamar yadda ya kamta.

Kwanakin baya ba da dadewa ba,kungiyar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya ta sanar da sabuwar takardar jerin sunayen nagartattun `yan wasa na duniya,shahararren maguji daga kasar Jamaica Asafa Powell ya zama na farko na maza,shahararriyar magujiyar gudun dogon zango daga kasar Habasha Meseret Defar ta zama ta farko ta mata.Game da wasan gudun tsallake shinge na mita 110 na maza kuwa,`dan wasa daga kasar Sin kuma zakaran taron wasannin Olimpic Liu Xiang da `dan wasa daga kasar Cuba Dayron Robles sun zama na farko baki daya.

Ran 19 ga wata,a gun zagaye na karshe na gasar rukunin C ta gasar kananan kungiyoyi ta gasar cin kofin Asiya ta shekarar 2007,kungiyar kasar Sin ta samu zama na uku a rukunin C,ba ta samu ikon sake shiga gasar ba.Kasashe hudu da suka hada da kasar Thailand da ta Vietnam da ta Malaysia da ta Indonesia ne suka shirya wannan gasar cin kofin Asiya tare,gaba daya kungiyoyi 16 suka halarci gasar,kuma za a yi zagaye na karshe na gasar a ran 29 ga wata.(Jamila zhou)