Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-24 21:21:11    
Kasar Sin tana gudanar da ayyukan sake yin amfani da tsoffin wayoyin salula

cri

Bisa sabuwar kididdigar da ma'aikatar sadarwa ta kasar Sin ta bayar, an ce, yanzu yawan mutanen da suke yin amfani da wayoyin salula a kasar Sin ya kai miliyan 480, shi ya sa kasar Sin ta zama kasa mafi girma wajen yin amfani da wayar salula a duk duniya. Gaggauta shigowar sabbin wayoyin salula na zamani ya sa yawan tsoffin wayoyin salula da aka daina yin amfani da su ya samu karuwa sosai. Haka kuma kullum a kan mayar da tsoffin wayoyin salula da kayayyakinsu a matsayin juji na zaman yau da kullum. Idan an binne tsoffin wayoyin salula da kuma batirorinsu, to sinadarin zinariya da mercury da lead da cadmium da ke cikinsu za su lalata kasa da kuma ruwan da ke karkashin kasa kai tsaye. Amma idan an kone su, to sinadarin da ke cikinsu zai gurbata iska, ta haka zai yi illa sosai ga lafiyar dan Adam.

Sabo da haka, kafa wani tsarin daidaitawa da kuma sake yin amfani da tsoffin wayoyin salula da chajar salula da kuma batirorinsu da dai sauran abubuwa marasa amfani bisa hanyar hadin gwiwar hada-hada da sayarwa da kuma yin amafani da su gaba daya ya zama wani abin gaggawa, haka kuma ita wata hanya ce mafi kyau wajen warware matsalar. Kamfanin wayar salula na kasar Sin, kamfani ne mafi girma na Sin a fannin ba da hidima ga kayayyakin sadarwa ya hada gwiwa tare da wasu muhimman kamfanonin samar da wayoyin salula kamar kamfanin Motorola da na Nokia wajen bayar da wani shirin kiyaye muhallin halittu wanda ake kiransa 'koren akwati'. Mataimakin shugaban kamfanin wayar salula na kasar Sin Sha Yuejia ya bayyana cewa,

"Sarrafa da tsoffin wayoyin salula da kuma sake yin amfani da su, ba kawai zai iya biyan bukatun kasar Sin wajen raya zaman al'umma tare da kyakkyawan muhalli ba, har ma zai iya biyan bukatun kasar Sin wajen raya zaman al'umma mai tsimin makamashi. Kamfanin wayar salula na kasar Sin ya yi alkawari cewa, zai ci gaba da kara karfin sake yin amfani da tsoffin wayoyin salula, kuma ya nuna maraba da kamfanonin samarwa da na sayarwa masu yawa da su sa hannu a cikin shirin kiyaye muhalli na koren akwati domin bayar da gudummowa ga kiyaye muhalli."

Bisa labarin da muka samu, an ce, ya zuwa yanzu an riga an fara aiwatar da wannan shiri a muhimman birane 40 na kasar Sin, kuma cibiyoyin sayarwa kusan 1000 na kamfanin wayar salula na kasar Sin, da kuma cibiyoyin sayarwa da gyare-gyare kusan 300 na kamfanonin Motorola da Nokia sun ajiye irin wannan koren akwati wajen karbar tsoffin wayoyin salula da kayayyakinsu.

Ana iya samun moriya a fannonin tattalin arziki da kuma zaman al'umma a cikin aikin sake yin amfani da tsoffin wayoyin salula. Mun ba da batir din wayar salula kamar misali, ko wanen batir yana kunshe da sinadarin cobalt gram 6, kuma yanzu yawan wayoyin salula da aka daina yin amfani da su a kasar Sin a ko wace shekara ya zarce miliyan 100. Idan ana iya samun tsoffin batirorin wayoyin salula miliyan 100 a ko wace shekara, to yawan sindarin cobalt da za a iya samu zai kai ton 600. Sabo da haka ana sa ran cewa, aikin samun tsoffin batirori zai zama tamkar wani ma'adinin zinariya da ke birane.

Domin kara rawar da shirin kiyaye muhalli na koren akwati ya taka, da kara fahimtar sinawa wajen kiyaye muhalli, da kuma jawo hankulan mutane masu yawa wajen sa hannu a cikin wannan shiri, kamfanin wayar salula na kasar Sin ya gayyaci sanannun masu masana'anatu da kuma 'yan wasa masu yawa wajen yin furofaganda. Teng Haibin, dan wasan tsalle-tsalle da lankwashe-lankwashe na kasar Sin wanda ya taba zama zakara a cikin wasannin Olympics yana daya daga cikinsu, kuma ya gaya wa wakilinmu cewa,

"ana yin kirari wajen shirya wani taron wasannin Olympics maras gurbata muhalli a birnin Beijing, shi ya sa a cikin shirin, an yi kira da a ajiye tsoffin wayoyin salula da batirorinsu a cikin irin wannan koren akwati domin sake yin amfani da su, ta yadda za a iya kiyaye muhallin halittu. Wannan harka tana da ma'ana sosai, bari mu sa hannu a cikin wannan shiri."

Yanzu, shirin kiyaye muhalli na koren akwati ya riga ya samu karbuwa sosai daga jama'a. Yue Wei, wani mazaunin birnin Beijing ya gaya mana cewa,

"a ganina, wannan harkar da kamfanin wayar salula na kasar Sin ya shirya tana da ma'ana sosai. Ina fatan mutane masu yawa za su iya nuna goyon baya ga ayyukan kiyaye muhalli, ta yadda birnin Beijing zai iya samun wata kyakkyawar makoma a nan gaba."(Kande Gao)