Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-23 15:44:31    
Wasu labaru game da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet

cri

Labarin farko shi ne, yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet ya kai fiye da miliyan 2 cikin shekara 1 da ta gabata. A ran 29 ga wata, ma'aikatar hanyar dogo ta kasar Sin ta bayar da labari, cewar tun daga ran 1 ga watan Yuli na shekarar bara zuwa karshen watan Yuni na shekarar da muke ciki, yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet ya kai miliyan 2 da dubu 20. A waje daya, yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu ta wannan hanyar dogo ya kai ton kimanin miliyan 11.

Wani babban jami'in ma'aikatar hanyar dogo ta kasar Sin ya bayyana cewa, bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet yau da shekara 1 da ta shige, hanyar dogo da injuna da na'urori da ma'aikata da fasahohin yin amfani da wannan hanyar dogo sun ci jarrabawar da sauye-sauyen yanayin duniya suka yi musu a cikin lokuta daban-daban. Ba a samu hadarurukan zirga-zirga ba, ba a samu aukuwar hadarin mutuwar ma'aikata ko fasinjoji a kan wannan hanyar dogo a cikin wannan shekara 1 da ta shige.

Bugu da kari kuma, an tsara manufofi masu tsanani iri iri bisa "Dokar Kiyaye Muhalli" da "Dokar Kiyaye Namun Daji" na kasar Sin domin kiyaye muhalli a kan hanyar dogo ta Qinghai-Tibet.

Wani labari daban shi ne yawan masu bin addinin Bhudda wadanda suke zuwa jihar Tibet domin aikin hajji yana ta karuwa

Bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet yau da shekara 1 da ta shige, yawan masu bin addinin Bhudda wadanda suke zuwa jihar Tibet domin aikin hajji yana ta karuwa.

Bisa kididdigar da gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta yi, an bayyana cewa, a cikin fadar Potala da dakin Ibada na Luobulinka da na Dazhao wadanda suke birnin Lhasa kawai, yawan masu bin addinin Bhudda da suka yi aikin hajji a shekarar da ta gabata ya kai dubu 328, wato ya karu da dubu 62 bisa na shekarar 2005.

Yawancin wadannan masu aikin hajji sun je jihar Tibet ne ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet. A waje daya, wasu 'yan kabilar Tibet sun je dakin Ibada na Tarsi da ke lardin Qinghai ne ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet.

Labarin kashe na yau shi ne an kafa tsarin jin kai a jihar Tibet

Tun daga ran 1 ga watan Yuli, an soma aiwatar da ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta a kauyukan jihar Tibet. Sabo da haka, ya zuwa yanzu, an riga an kafa kwarya-kwaryar tsarin jin kai da ke bisa tushen tabbatar da zaman rayuwar jama'a da na samar da wurin kwana da jiyya da ilmi ga mazaunan jihar domin tabbatar da zaman rayuwar jama'ar jihar.

Bisa wannan tsari, gidan da yawan kudin shiga da kowane iyalansa bai kai kudin Renminbi yuan dari 8 a kowace shekara zai shiga wannan tsari. Sabo da haka, manoma da makiyaya dubu 230 wadanda suke fama da talauci sosai za su samu moriya daga wannan tsari.

Ya zuwa karshen shekarar 2006, yawan mazaunan biranen jihar da ake samar musu kayayyakin jin kai ya riga ya kimanin dubu 44. Ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta ya kai kudin Renminbi yuan 130 a kowane wata a shekarar 1997, amma yanzu wannan adadi ya riga ya kai kudin Renminbi yuan 230 a kowane wata.

Bugu da kari kuma, jihar Tibet tana kokarin kafa wani sabon tsarin jin kai da zai dace da bunkasuwar tattalin arziki da zaman rayuwa na jihar, kuma zai shafi dukkan mazaunan jihar, kuma zai shafi fannoni daban-daban.(Sanusi Chen)