 Chen Jiangwen, wani jami'in soja na rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin da ke Liberia, ya bayyana jiya Lahadi cewa, a ran 20 ga wata, tawagar musamman da MDD ta tura zuwa Liberia ta bayar da babbar lambar yabo ta MDD ga kungiyar likitoci ta rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta Sin da ke Liberia, don nuna yabo a kan kyakkyawan aikinsu a wajen kiyaye zaman lafiya.
A cikin jawabinsa, manzon musamman na babban sakataren MDD da ke a kasar Liberia, Alan Doss ya nuna babban yabo kan kyakkyawar rawar da sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin suka taka. Ya ce, kiyaye zaman lafiya a Liberia nauyi ne babba, amma kungiyar likitoci ta Sin ta ba da babban taimako wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar da kuma farfado da ita, kuma ya yi alfaharin irin nasarorin da sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin suka samu.(Lubabatu)
|