Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-22 17:49:57    
Sojojin kasar Sin sun je kasar Rasha domin halartar rawar daji

cri

A ran 21 ga wata, sojojin karshe na kasar Sin wadanda za su halarci rawar daji ta "Zaman lafiya-2007" da dakarun kasashen kungiyar hada kai ta Shanghai za su yi tare domin yin yaki da 'yan ta'addanci sun tashi daga birnin Turfan na jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin zuwa yankin yin rawar daji da ke jihar Chelyabinsk ta kasar Rasha ta hanyar dogo.

Sufurin sojoji da kayayyaki ta hanyar dogo muhimmiyar hanya ce da ake bi domin rawar daji ta "zaman lafiya-2007" da za a yi. Ban da sojoji da ma'aikatai, ana kuma sufurin na'urori da kayayyaki na soja ta hanyar dogo. Manjo-janar Li Weiping na rundunar sojan kasar Sin ya bayyana cewa, sufurin sojoji da kayayyakin soja ta hanyar dogo da ake yi a wannan karo wani babban cigaba ne mai ma'anar tarihi a kan tarihin sufurin sojoji da kayayyakin soja na kasar Sin, rundunar soja ta 'yantar da jama'a ta kasar Sin za ta iya samun fasahohi masu daraja daga wannan aiki a nan gaba.

Za a yi rawar daji ta "Zaman lafiya-2007" ne tun daga ran 9 zuwa ran 17 ga watan Agusta mai zuwa a birnin Urumqi na kasar Sin da shiyyar Chelyabinsk ta kasar Rasha. Sojojin kasashen Sin da Khazakstan da Kirkistan da Rasha da Tajikstan da Uzebikstan za su halarci wannan rawar daji tare. (Sanusi Chen)