Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-20 18:24:59    
An samu ra'ayi iri daya a fannoni hudu a gun shawarwarin zagaye na shida tsakanin shugabannin kungiyoyin wakilai a nan Beijing

cri

An kawo karshen taron shugabannin kungiyoyin wakilai a gun shawarwarin zagaye na shida tsakanin bangarori shida kan batun nukiliyar Korea ta Arewa yau Jumma'a a nan birnin Beijing. Wata sanarwar da aka bayar bayan taron ta ce, bangarori daban-daban sun samu ra'ayi iri daya a fannoni hudu bisa manyan tsare-tsare kan ayyukan nan gaba, sun kuma amince da daukar matakai uku don tabbatar da wannan ra'ayi.

Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Mr. Wu Dawei ya yi jawabi a gun bikin rufe taron, inda ya furta cewa bangarori daban-daban sun samu ra'ayi iri daya a fannoni hudu cikin halin girmama wa juna da yin shawarwari bisa matsayin daidaici. Ya fadi cewa:   'Bangarori daban-daban sun yi shawarwari har sun kulla yarjejeniyar muhimman tsare-tsare cikin sakin jiki kan ayyukan nan gaba domin kokarin tabbatar da rashin kasancewar makaman nukiliya a Zirin korea, da maido da dangantakar dake tsakanin kasashen da abun ya shafa da kuma shimfida zaman lafiya mai dorewa a arewa maso gabashin Asiya ' . Sa'annan Mr. Wu Dawei ya bayyana cewa, ra'ayi iri daya a fannoni hudu shi ne, bangarori daban-daban sun sake alkawarta sauke nauyin dake bisa wuyansu na aiwatar da abububwan da aka tanada cikin sanarwar hadin gwiwa ta ran 19 ga watan Satumba da kuma takardar hadin gwiwa ta ran 13 ga watan Fabrairu ; Sa'annan bangaren Korea ta Arewa ya sake alkawarta sauke alhakin dake bisa wuyansa na gabatar da dukan shirye-shiryensa na bunkasa makaman nukiliya da kuma lalata kayayyakin nukiliya da yake da su wajen harhada makaman nukiliya ; bugu da kari za a bai wa bangaren Korea ta Arewa mai mai nauyi na Ton 950,000 da sauran taimakon jin kai. Ban da wannan kuma Mr. Wu Dawei ya shelanta cewa, kafin karshen watan gobe, za a kira tarurrukan kungiyar aiki mai kula da harkokin rashin kasancewar makaman nukiliya a Zirin Korea, da kungiyar aiki mai kula da harkokin maido da huldar dake tsakanin kasashen Korea ta Arewa da Amurka,da kungiyar aiki mai kula da harkokin maido da huldar dake tsakanin kasashen Korea ta Arewa da Japan, da kungiyar aiki mai kula da harkokin tattalin arziki da makamashi da kuma na kungiyar aiki mai kula da harkokin shimfida zaman lafiya da kafa tsarin tsaro a arewa maso gabashin Asiya.

    Mr. Yang Mingjie, shugaban hukumar nazari a fannin tsaro da muhimman tsare-tsare ta kasar Sin ya yi hasashen cewa :  'A ganina, an samu sakamako mai gamsarwa a wasu fannoni a gun taron , musamman ma a fannoni biyu, wato fanni na farko shi ne, bangaren Korea ta Arewa ya sake alkawarta sauye nauyin dake bisa wuyansa na lalata kayayyakin nukiliya da yake da su wajen harhada makamai ; fanni na biyu shi ne, bangaren da abin ya shafa ya bai wa Korea ta Arewa mai mai nauyi na Ton 950,000 da kuma sauran taimakon jin kai'.

Game da makomar yunkurin shawarwarin tsakanin bangarori shida, Mr. Yang Mingjie ya furta cewa:  Batun nukiliyar Korea ta Arewa ba wai wani batun nukiliya da batun daina yaduwar makaman nukiliya da kuma batun kayyade yawan sojoji kawai ba, a zahiri dai, batu ne dake shafar dangantakar dake tsakanin kasashen Amurka da Korea ta Arewa, da shirye-shiryen da za a yi a Zirin Korea bayan yakin cacar baki da kuma aikin kafa tsarin tsaro da shimfida zaman lafiya a arewa maso gabashin Asiya.

A karshe dai, Mr. Yang ya ce, kila za a gamu da wassu matsaloli a duk tsawon yunkurin daidaita batun nukiliyar Korea ta Arewa, amma ko shakka babu bangarori daban-daban za su ci gaba da yin kokari wajen daidaita wannan batu kamar yadda ya kamata, ta yadda za a cimma burinsu na tabbatar da dukan matakan da aka dauka a gun wannan taron shugabannin kungiyoyin wakilai da aka gudanar a nan Beijing. ( Sani Wang )