Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-20 15:36:12    
An soma aiwatar da shirin daukar kwararru a nan Beijing domin taron wasannin Olympic

cri

Aminai 'yan Afrika, sanin kowa ne, gudanar da wani gagarumin taron wasannin Olympic cikin nasara na dogaro da samun ingantattun filaye da dakunan wasanni na zamani da kuma kyakkyawan tsarin zirga-zirga da kuma wani rukunin kwararru da za su yi hidimomi domin taron wasannin Olympic. A lokacin da ya rage shekara daya da 'yan watanni kawai don kiran taron wasannin Olympic na yanayin zafi na 29 na shekarar 2008 a nan birnin Beijing, a kwanakin baya dai, gwamnatin birnin Beijing ta yi shelar aiwatar da " Shirin daukar kwararru domin taron wasannin Olympic".

An bayyana, cewa makasudin yunkurin aiwatar da shirin daukar kwararru domin taron wasannin Olympic, shi ne domin bada tabbaci ga cimma manufar taron wasannin Olympic, da samar da gudummowar da ta wajaba ta fannin kwararru da kuma tafiyar da harkokin kwararru gwargwadon iyawa a duk tsawon lokacin share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing da kuma yin amfani da wannan kyakkyawar damar yin aikin share fage domin shiryawa da horaswa da kuma adana wassu kwararru.

Bisa bukatun taron wasannin Olympic, wannan shirin daukar kwararru ya tabbatar da muhimman ayyuka guda 16 na raya rukunin kwararru a fannin harkokin waje, da tsaro da zirga-zirga da kuma na kiyaye muhalli da dai sauran fannoni. Mr. Xin Tieliang, shugaban hukumar kula da harkokin tubewa da nadawa ta birnin Beijing ya yi nuni da ,cewa gwamnatin birnin za ta bada taimakon kudi wajen aiwatar da wannan shiri.

Har kullum akan mayar da hankali sosai kan batun tsaro na taron wasannin Olympic. Abun da ya fi janyo hankulan mutane shi ne, wadanne mutane ne za su bada tabbaci ga samun kyakkyawan tsaro na taron wasannin Olympic. Game da wannan dai, shirin daukar kwararru domin taron wasannin Olympic na bukatar hukumar kula da tsaro ta birnin Beijing da ta raya wani rukunin kwararruda yawansu ya kai kimanin 12,000 wadanda suka kware a fannin daidaita matsalolin ba-zata tun da wuri. Mr. Shan Zhigang, daraktan ofishin siyasa na hukumar tsaro ta birnin Beijing ya furta, cewa suna mai da hankali sosai kan aikin mu'amala tare da kasashen ketare a fannin horar da kwararru domin taron wasannin Olympic. Ya kuma kara da, cewa " a halin yanzu, kimanin kashi 50 cikin kashi 100 na 'yan sandan hukumar sun samu digirin ilimi ta hanyar yin jarrabawa a fannin harsunan waje. A 'yan shekarun baya, mun tura dalibai sama da 400 zuwa Jami'ar Westminster ta Burtaniya da kuma Jami'ar Canberra ta Australiya domin samun digirin Master. Da yake daliban sun yi kokari matuka wajen karatu a kasar Burtaniya, shi ya sa suka uyi alfaharin samun damar ganawa da sarauniyar kasar. Ta wannan hanya ce muka habaka musanye-musanye tare da hukumomin 'yan sanda na kasashen duniya, da kara samun fasahohin gudanar da manyan harkokin kasa da kasa, da kuma yin koyi da fasahohi na zamani da hukumomin 'yan sanda na biraren da suka taba daukar nauyin gudunar da taron wasannin Olympic."

Za a yi tsaro sosai da sosai ne domin tabbatar da samun kwanciyar hankali ga baki daga wurare daban-daban na duniya. To, wadanne mutane ne za su taryi masu yawon shakatawa da za su zo nan Beijing domin kallon wasannin Olympic? Bisa bukatun shirin daukar kwararru, hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta birnin Beijing za ta kula da aikin horar da wadanda za su tafiyar da harkokin yawon shakatawa da kuma wasu kwararru na sana'ar musamman ta yawon shakatawa, wadanda za su yi hidimomi ga taron wasannin Olympic na Beijing.

Aminai 'yan Afrika, a duk tsawon lokacin da ake gudanar da wannan gagarumin taro, za a iya ga mutane masu aikin sa kai ko'ina a nan birnin Beijing. Wani taron wasannin Olympic da akan gudanar cikin nasara na da nasaba da namijin kokari da kwararrun mutane mafi nagarta sukan yi; A lokaci daya, wani gagarumin taron wasannin Olympic da akan gudanar cikin nasara, labuddah zai samar da kyakkyawar damar samun ci gaba ga mutane mafi nagarta.( Sani Wang )