A yayin da yake hira da manema labarai kuma, mataimakin shugaban sashen yaki da bala'i na ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin, Pang Chenmin ya bayyana cewa, tabbatar da zaman rayuwar jama'ar da bala'in ya shafa yadda ya kamata, ya kasance babban nauyin da ke bisa wuyan hukumomin kula da harkokin jama'a. Ya ce,"Tabbatar da zaman rayuwar jama'ar da bala'in ya shafa yadda ya kamata, babban nauyi ne da ke bisa wuyanmu. Mun bukaci hukumomi na matakai daban daban da su tabbatar da ba da agaji yadda ya kamata ga jama'a cikin awa 24 a kowace rana, wato a tabbata suna da ruwan sha da kuma rigunan sanyawa da kuma wuraren kwana na wucin gadi da kuma magunguna."
Malam Zhang Zhifu, wani manomin da muka ambata a baya, ya fito ne daga yankin karkatar da ambaliyar ruwa ta Mengwa. An dai fara aiki na wannan yanki wajen karkatar da ambaliyar ruwa a ranar 10 ga watan nan da muke ciki, kuma kawo ranar 18 ga watan, kudaden agaji da suka kai kudin Sin yuan dubu 710 da kuma shimkafa da ruwan sha da taliya da kwal da dai kayayyakin agaji sun riga sun zo hannun jama'ar wurin. Bayan haka, an kuma tura kungiyoyin jiyya sama da 130 zuwa kauyuka daban daban na yankin, don ba da magunguna da kuma samar da jiyya ga jama'ar wurin. Bayan haka, don samar da saukin tafiya ga jama'ar wurin, an kuma ba da jiragen ruwa ga kowane kauye. Hanyoyin samar da lantarki da suka lalace a lokacin ambaliyar ruwa ma, an gyara su yadda ya kamata, don samar da wutar lantarki ga jama'ar da bala'in ya shafa yadda ya kamata.
1 2 3
|