Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-18 17:24:14    
Kasar Libya ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga masu aikin jinya 6 na kasashen waje

cri

Ran 17 ga wata da dare, kwamitin koli na shari'ar kasar Libya ya yi taro a Tripoli, babban birnin kasar, bayan taron, ya bayar da wata sanarwa inda ya sanar da cewa, ya yanke hukuncin daurin rai da rai maimakon hukuncin kisa ga nas-nas 5 na kasar Bulgaria da wani likita na Palesdinu wadanda aka zarga da laifin cusa kwayoyin cutar AIDS wa yara a Benghazi na kasar Libya.

Ko da yake a cikin sanarwar ba a ce ko wadannan mutane 6 da aka tsare su na tsawon shekaru za su cigaba da zama a gidan wakafi a kasar Bulgaria bayan da aka komar da su, amma saboda akwai yarjejeniyar mayar masu laifuffuka, an yanke hukuncin daurin rai da rai maimakon hukuncin kisa ya kawo makoma ga wadannan mutane 6.

Bisa shiri, ya kamata a yi shawarwari a ran 16 ga wata da dare, amma wannan kwamitin koli na shari'a ya yi ta dakatar da yin hukunci ga wannan magana, ya zuwa ran 17 ga wata da dare an yanke hukuncin karshe. Bisa maganar da wani jami'in gwamnatin kasar Libya ya yi, dalilin da ya sa aka dakatar da yin hukunci sau da yawa shi ne saboda mutanen da aka jikkata ko iyalansu a batun Benghazi ba su sami duk diyya da daddale wasu yaejejeniyoyi ba. Ya zuwa yammancin ran 17 ga wata, kakakin mutanen da aka jikkata ya ba da tabbacin cewa, an riga an cika bukatan biyan diyya da iyalan mutane 460 da aka jikkata suka gabatar, ko wane iyali zai sami diyya na dolar Amurka miliyan daya, daga baya, sun gabatar da kwamitin koli na shari'a ba su bukata a yanke hukuncin kisa ga mutane 6 da aka zargi da laifin cusa kwyoyin cutar AIDS ba. Saboda haka, a wannan rana da dare, kwamitin koli na shri'a na kasar Libya ya mai da hukuncin kisa ya zama daurin rai da rai ga ma'aikatan jinya 6.

Batun cusa kwayoyin cutar AIDS ya faru ne a karshen shekarar 90 na karni na 20. a lokacin can, yara 438 da ke cikin wani asibitin yara na Benghazi sun kamu da kwaoyoyin cutar AIDS, ya zuwa yanzu, yara 56 daga cikinsu sun mutu. Kuma an zargi 'yan nas-nas 5 na kasar Bulgaria da wani likitan Palesdinu da laifin haddasa haka, an kama su a farkon shekarar 1999, kuma suna gidan kurkuku har zuwa yanzu. Ko da yake wadannan mutane 6 suna ta cewa ba su ji ba kuma ba su gani ba, amma kotun yankin Benghazi ta yanke hukuncin kisa a kan su a watan Mayu na shekarar 2004. kuma a ran 11 ga wannan wata, babban kotun kasar Libya ta tabbatar da hukuncin kisan.

Amma, saboda kwamitin koli na shari'a shi ne hukumar koli kan harkokin shari'a ta kasar Libya, shi ya sa, wannan ya zama dama ta karshe da aka canja hukucin kisan.

Yanzu, kwamitin koli na shari'a na kasar Libya ya mai da hukuncin kisan da ya zama daurin rai da rai, wannan ya kwantar da hankalin mutanen da suke mai da hankulansu kan makomar wadamman ma'aikatan jinya 6. Amma, masu bincike suna ganin cewa, da ma bai kamata a nuna damuwa kan wannan batu ba, saboda kwamitin koli na shari'a na kasar Libya zai yanke hukunci kamar haka ko ba dade ka ba jima. Sun ce, tun bayan da shugaba Al-Qadhafi na kasar Libya ya yi watsi da nazarin makaman kare dangi, kuma yana son kasar Libya ta koma cikin sauran kasashen duniya, kullum kasar Libya tana kokarin daddale yarjejeniya tare da kasar Amurka, da kungiyar gammayar kasashen Turai da kuma kasar Bulgaria kan batun cusa kwayoyin cutar AIDS na Benghazi. Shi ya sa kasashen Libya da Bulgaria suka kafa wani kwamitin asusun Benghazi na kasa da kasa a karkashin taimakon kasar Amurka da kungiyar EU domin biyan diyya ga yaran da aka jikkata ko iyalansu. Da zarar a biya duk diyya, ko shakka babu an canja hukuncin kisa.

Ban da haka kuma, masu bincike suna ganin cewa, canja hukuncin kisa ga wadannan ma'aikatan jinya 6 ya kawo kyakkyawar makoma ga batun Benghazi wanda kasashen Libya da Bulgaria ke damuwa da shi a cikin dogon lokaci a baya, kuma mai yiyuwa ne wadannan mutane 6 za su sake samum 'yancinsu. A sa'I daya kuma, wannan zai kyautata huldar da ke tsakanin kasar Libya da kasar Amurka da kungiyar EU, wannan zai cire wani shinge ga kasar Libya wajen gudun takunkumin da kasashen Turai ke kakkaba mata a cikin dogon lokaci da kuma kasar Libya ta sake koma wa cikin al'ummar kasashen duniya. [Musa Guo]