Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-18 16:58:04    
Wani iyalin kasar Sin na sassaka mutum mutumi da fasahohinsu

cri

Malam Xu Zhucu mai shekaru 68 da haihuwa shi ne babban malamin da ya yi suna sosai a kasar Sin wajen sassaka mutum mutumi, mutum mutumin da ya sassaka kuma aka rada musu sunan Xu Zhucu sun zama wata shaharariyyar alamar mutum mutumin da aka fi son tanadinsu. Dukkan Kakani-kakanin Mr Xu Zhucu su ne masu sassaka mutum mutumi. A shekarar da muke ciki, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta tabbatar da cewa,Mr Xu Zhucu shi ne mai gadon aikin sassaka mutum mutumi da ke iya wakiltar masu sassaka mutum mutumin kasar Sin, dansa mai suna Xu Qiang shi ma mai fasaha ne na tsara fasalin mutum mutumi. Mr Xu Zhucu ya bayyana cewa, iyalin Xu suna da wani dakin nuna fasahar mutum mutumi wanda shi kadai kawai a kasar Sin, dakin yana garinsa da ke birnin Zhangzhou na lardin Fujian a bakin teku na kudu maso gabashin kasar Sin, kuma an rada masa suna da sunan Mr Xu Zhucu da cewa, "Dakin nuna fasahar mutum mutumi ta Xu Zhucu na Zhangzhou". Da aka shiga dakin, sai nan da nan aka iya ganin mutum mutumin da aka sassaka da samfurorinsu suke yi kama da tsofaffin da ke da gemu mai launin fari, da kuma mutum mutumin da suka yi kama da masu nuna wasan ban dariya tare da masu nuna wasannin kwaikwayo da shahararrun mutanen tarihi da sauransu irin na kananan mutum mutumi wadanda suke iya motsi da idanunsu da girarsu da bakunansu da hanayensu da kofafinsu , sa'anan kuma bisa taimakon mutane ne, suka iya nuna wasanni iri iri daban daban.

Yawancin mutum mutumi su ne mutum mutumin da aka sassaka da katako, amma mutum mutumin Xu Zhucu su ne kananan da aka iya sanya su cikin jakar da aka dinki da zawwati, Mr Xu Zhucu ya bayyana cewa,mutum mutumin da aka iya sanya a cikin jakar da aka dinki da zawwati kanana ne, duk saboda an yi baya baya wajen zirga-zirgar ababen hawa a da a birnin Zhangzhou, za a iya sanya mutum mutumi a cikin jakar da aka rataya a jikin mutane, wato za a iya saukin tafiya ke nan.

An yi kyau da sassaka kananan mutum mutumi, amma a lokacin da sassaka su, a iya gamu da wahaloli da yawa , dole ne a sassaka wani dan katako don ya zama kawunan mutum mutumi da dai sauransu, kuma dole ne su yi kama da mutanen gaskiya sosai da sosai, sa'anan kuma za a shafa musu fenti, a goge su don su yi santsi sosai tamkar yadda tangaram suke yi, muhimmin abu shi ne a mayar da su don su zama wadanda ke iya yin abubuwan da mutane suke yi tamkar yadda suke da rai. Mr Xu Zhucu ya bayyana cewa, in ana son sassaka mutum mutumi da kyau, dole ne a sassaka samfurorinsu tamkar yadda suke da rai. An sassaka mutum mutumi da kadako, amma katako ba shi da rai, amma ya kamata a mai da hankali sosai ga sassaka su da suke yin motsi tamkar yadda suke da rai.

Iyalin Xu suna aikin sassaka mutum mutumi daga zuri'a zuwa zuri'arsu. Mr Xu Zhucu yana cikin zuri'ar Xu ta 6. Tun lokacin da ya cika shekaru goma da haihuwa, ya soma koyon sassaka mutum mutumi. A lokacin da yake karami, ya yi kokarin koyon fasahar sassaka, har ma ya lalata dukkan danyun katakon da ake tanadi a gidansa. A lokacin da ya cika shekaru 16 da haihuwa, ya shiga gasar da aka shirya wajen nuna fasahar sana'o'I da hannu. Ya sami lambar yabon musamman, har ma an yi amfani da mutum mutumin da ya sassaka don su zama kyaututuka ga shugabannin kasashen waje da suka kai ziyara a kasar Sin. Ya zuwa yanzu, ya riga ya sassaka mutum mutumin da yawansu ya kai ire-ire fiye da 600, kuma an yi nuninsu a kasashen waje fiye da 100. a bara, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta shigar da mutum mutuminsa cikin rukunin farko na sunayen abubuwan tarihi na al'adun kasar Sin ba na kayayyaki ba . An kuma mayar da shi don ya zama mai gado da ke iya wakiltar rukunin masu sassaka mutum mutumi na kasar Sin.

Dansa mai suna Xu Qiang shi ne mai sassaka mutum mutumi. Tun lokacin da yake karami, ya soma koyon fasahar sassaka mutum mutumi daga wajen mahaifinsa Mr Xu Zhucu, yanzu ya riga ya zama shugaban dakin nuna fasahar sassaka mutum mutumi na Xu Zhucu na birnin Zhangzhou, ya ce, yanzu, ya mai da hankali sosai ga sassaka mutum mutumi domin biyan bukatun masu yawon shakatawa, kuma yana son sassaka kayayyakin wasa domin yara tare da samfurorinsu da yawa don biyan bukatun kasuwannin zamanin yau.(Halima)