Ran 11 ga wata, wani jami'in kula da ayyukan taron wasannin Olympic na Beijing ya bayyana cewa, an riga an kammala gina muhimman gine-gine na yawancin filaye da dakunan wasa domin taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008. A gun taron manema labaru da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya shirya a wannan rana, malam Wu Jingjun, babban injiniya na ofishin ba da jagorancin ayyukan da ke shafar taron wasannin Olympic na shekarar 2008, ya bayyana cewa, an riga an fara gina filaye da dakunan wasa guda 31 da gine-gine guda 5 da abin ya shafa, a ciki kuma an kammala gina filin wasa na wasan kwallo mai laushi na Fengtai a shekarar bara. Yanzu an kawo karshen gina muhimman gine-gine na yawancin filaye da dakunan wasa, ana yin musu ado da ajiye injunan wutar lantarki, ana kusan gama wasu ayyukan. Bayan labaru, za mu kawo muku wani bayanin musamman kan wannan fanni.
Ran 15 ga wata, a gun gasar ba da babbar kyauta ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje da Hadaddiyar kungiyar wasan tsalle-tsalle da guje-guje wato IAAF ta shirya a birnin Sheffield na kasar Birtaniya, dan wasa Liu Xiang na kasar Sin ya sami lambar zinariya a gun gasar gudun ketare shine mai tsawon mita 110 ta maza da dakikoki 23 da motsi. Wannan ne karo na farko da Liu Xiang ya zama zakara a cikin gasar wasan tsalle-tsalle da guje-guje da aka yi a filin wasa a kasar Birtaniya. 'Yan wasa Wilson Ryan da Moore Anwar na kasar Amurka sun zama na biyu da na uku a gun gasar.
An kammala gasar wasan kwallon kafa ta mata ta kasa da kasa da aka yi bisa gayyata a birnin Shenyang na arewacin kasar Sin a ran 10 ga wata. A cikin karon karshe da aka yi, kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Mexico da ci daya da ba ko daya, ta taka, ta zama zakara a wannan karo. Kungiyar kasar Italiya ta zama ta uku saboda ta lashe kungiyar kasar Thailand da cin 2 da 1.
Tun daga ran 10 zuwa ran 15 ga wata, a birnin Chengdu da ke kudu maso yammacin kasar Sin, an yi gasar fid da gwani ta wasan kwallon badminton ta kasar Sin. A cikin dukkan kananan gasanni 5 da aka yi, 'yan wasan kasar Sin sun sami lambobin zinariya a cikin kananan gasanni 4, 'yan wasan kasar Indonesia mata sun zama zakara a cikin gasa ta tsakanin mata biyu biyu kawai.(Tasallah)
|