An yi bikin rufe taron kasa da kasa kan batun Darfur na kasar Sudan a Tripoli, hedkwatar kasar Libya. Taron ya samar da bakin zaren warware rikicin Darfur na kasar Sudan .
Da farko, taron ya amince da amfanin jagorancin da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar kasashen Afrika da kasashen da ke kewayen kasar Sudan suka ba da ga daidaita batun Darfur . Taron ya bayar da wata sanarwa a lokacin da aka rufe shi, inda ya nuna yabo ga kokarin da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar tarayyar kasashen Afrika da Libya da Masar da sauran kasashen da ke kewayen kasar Sudan suka yi don cim ma burin samun zaman lafiya da sake neman sulhuntawar siyasa. Kuma ya kirayi wadannan kungiyoyin kasa da kasa da kasashen da ke kewayen kasar Sudan da su ci gaba da neman samun daidaituwa sosai da gwamnatin Sudan da shugabannin kungiyoyi daban daban masu yin adawa da gwamnati da wakilan 'yan gudun hijira, kuma su zama babbar hanyar da ake bi wajen yin cudanya a tsakanin bangarori dadan daban da abin ya shafa na kasar Sudan don neman fahimtar ra'ayoyinsu da matsayinsu wajen yin shawarwarin zaman lafiya a kan batun Darfur. Sanarwar ta kirayi bangarorin siyasa da ba su rattaba hannu kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a Darfur ba da su halarci taron share fage ga shawarwarin shimfida zaman lafiya da za a yi a kasar Tanzaniya daga ranar 3 zuwa ranar 5 ga watan Augusta, kuma ta nemi bangarori daban daban da suke da nasaba da batun Darfur na kasar Sudan da su yi shawarwari sosai a kan lokacin da ya dace da shirya shawarwarin zaman lafiya da inda za a yi shi. Sanarwar ta kuma nemi shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afrika da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da su bayar da goran gayyata ga wakilai daban daban da za su halarci shawarwarin a karshen watan Augusta.
Sa'anan kuma, taron ya sa kaimi ga dukkan kungiyoyi masu yin adawa da gwamnati na shiyyar Darfur da su sami matsayi daya don yin shawarwarin shimfida zaman lafiya da gwamnatin Sudan cikin tsanaki tare da samun sakamako sosai. Yanzu gwamnatin Sudan ta riga ta bayyana fatanta na bude kofar shawarwari ga dukkan kungiyoyin masu yin adawa da ita wadanda suke son cim ma burin shimfida zaman lafiya a shiyyar Darfur, har zuwa ranar da aka rattaba hannu a kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a shiyyar daga dukan fannoni.
Na uku, taron ya nuna maraba da yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar tarayyar kasashen Afrika da gwamnatin Sudan suka rattaba hannu a kai game da jibge rundunonin sojojin hadin guiwa na kiyaye zaman lafiya da sauran batutuwa, kuma ya nemi bangarori daban daban da abin ya shafa da su dakatar da bude wutar yaki a shiyyar Darfur nan da nan da kawo karshen hargitsin yin adawa da juna a tsakaninsu da halartarsu a cikin gudanarwar neman sulhuntawar siyasa har zuwa ranar daddale yarjejeniyar siyasa ta kawo karshen rikicin daga dukan fannoni. Taron ya bayyana sosai cewa, jibge rundunonin sojojin hadin guiwa na kiyaye zaman lafiya a shiyyar Darfur zai ba da taimako ga kawo karshen hali mai zafi da ake ciki a shiyyar da kuma mayar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da cim ma buri na shimfida zaman lafiya daga dukkan fannoni, har ma zuwa ranar kawo karshen masifar jinkai da mazaunan shiyyar suke fama da ita cikin shekaru hudu ko fiye.
Game da taron duniya da aka yi kan batun Darfur, bangarori daban daban da abin ya shafa dukansu sun nuna yabo a kai sosai . A lokacin da yake jawabi, wakilin musamman na kasar Sin kan batun Darfur Mr Liu Gui ya nuna goyon baya ga matukar kokarin da kungiyar tarayyar kasashen Afrika da Majalisar Dinkin duniya da kasashen da ke kewayen kasar Sudan suka yi wajen daidaita batun Darfur.
A cikin jawabin da ya yi a gun bikin rufe taron, manzon musamman na kungiyar tarayyar kasashen Afrika Mr Salim Ahmed Salim ya karfafa cewa, taron ya ba da tasiri mai muhimmanci sosai ga Darfur da kuma dukan kasar Sudan, ya bayyana cewa, lokaci ya yi da za a sake yin shawarwarin shimfida zaman lafiya da aiwatar da shirin gudanar da harkokin siyasa bisa taswirar da aka tsara.(Halima)
|