Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-17 15:33:53    
Masu ciki da suke shan taba suna fuskantar barazanar haifi jarirai sirara

cri

Yanzu za mu soma gabatar muku da labarin da muka shirya muku. Nazarin da kwalejin nazarin kimiyyar kiwon lafiya na kasar Japan ya yi ya shaida cewa, masu ciki da suke da al'adar shan taba suna kara fuskantar barazanar haifi jarirai sirara da nauyinsu ba ya da yawa, in an kwatanta da wadanda ba su sha taba ba.

Jaridar 'Mainichi' ta kasar Japan ta ba da labari a kwanan baya cewa, ma'aikatar kiwon lafiya da harkokin 'yan kwadago ta kasar Japan ta yi bincike kan halin da jarirai suke ciki a fannin girmansu a shekarar 1990 da ta 2000, ofishin kiwon lafiyar mama da yaransu na kwalejin nazarin kimiyyar kiwon lafiya na kasar Japan ya sami sakamakon da aka ambata a baya, bayan da ya nazarci adaddin da abin ya shafa a kwanan baya. Jariran da nauyinsu ba ya da yawa suna kara fuskantar barazanar yiwuwar kamuwa da ciwon sukuri da sauran ciwace-ciwace, in an kwatanta su da jarirai wadanda suke koshin lafiya.

A cikin wadannan bincike sau 2 da aka yi a shekarar 1990 da ta 2000, an gano cewa, yawan masu ciki da suke da al'adar shan taba ya karu daga kashi 6.5 cikin kashi dari na shekarar 1990 zuwa kashi 10.9 cikin kashi dari na shekarar 2000. Yawan masu ciki da suke shan taba, kuma suka haifi jariran da nauyinsu ba ya da yawa ya kai kashi 11 cikin kashi dari a shekarar 2000, wanda ta yi daidai da na shekarar 1990. A cikin nazarin da aka yi, an ce, masu ilmin kiwon lafiyar mama da yaransu sun mayar da jariran da aka haife su ba da dadewa ba da nauyinsu bai kai gram dubu 2 da dari 5 ba a matsayin jariran da nauyinsu ba ya da yawa.

Bayan da aka yi la'akari da sanadan shekarun masu ciki da haihuwa da kuma makonnin da suka yi suna da ciki da dai sauransu tare, masu ilmin kiwon lafiyar mama da yaransu suna ganin cewa, yawan masu ciki da suke da al'adar shan taba da suka haifi jararan da nauyinsu ba ya da yawa, wato nauyinsu bai kai gram dubu 2 da dari 5 ba, ya ninka sau 2.2, in an kwatanta su da masu ciki wadanda ba su sha taba ba.

Saboda haka, a ganin masu ilmin kiwon lafiyar mama da yaransu, ya fi kyau masu ciki da suke da al'adar shan taba su yi watsi da wannan mummunar al'ada, in suka yi la'akari da yaransu.(Tasallah)