Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-17 15:00:28    
Ministan harkokin wajen Sudan ya jinjinawa huldar dake tsakanin kasarsa da Sin

cri

KHARTOUM. Ministan harkokin wajen kasar Sudan, Lam Akol , a ranar Litinin din nan ya yabawa irin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasarsa da kasar Sin da kuma irin goyon bayan da Sin ke bayarwa Sudan wajen tattaunawar kasa da kasa kan batutuwan da suka shafi Sudan.  Ministan ya fadi haka ne a wajen wani taron 'yan jaridu da aka yi bayan kammala wani taron wakilan da za su rufa baya wa mataimakin shugaban kasar Sudan na farko Salva Kiir Mayardit a ziyarar da zai kawo nan kasar Sin nan da dan lokaci mai zuwa.

Ziyara a cewar ministan na da muhimmanci idan aka yi la'akari da batun huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Ya ce taron tawagar, ya tattauna ne kan batutuwan da bangarorin za su tattauna a lokacin ziyarar da ke da nufin bunkasa hulda tsakanin Sin da Sudan.wadda Sudan ke fatan ganin ta sami nasara.

Ana sa ran cewar tawagar za ta yi bayani wa mahukuntan Beijing irtn halin da ake ciki a Sudan musamman kan batun shimfida zaman lafiya na yankin Darfur da kuma irin rawar da kasar Sin za ta taka wajen sake farfado da kasar.

A halin da ake ciki, ministan harkokin makamashi da ma'adinai na Sudan Awad Al- Jaz ya jaddada kudurin Kasar Sudan na kyautata hulda da kasar Sin musamman ma a fannin zuba jari da kuma yin hadin guiwa domin ayyukan hade arewaci da kudancin kasar ta Sudan.

Ministan ya cigaba da cewar ziyarar da mataimakin Shugaban kasar ta Sudan zai yi za ta kasance wani mabudi ne da kuma sauyin irin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Ana dai sa ran cewar mataimakin shugaban kasar na farko zai soma ziyarar aiki ne ta farko a kasar Sin wadda za ta shafe kwanaki shida yana yi. (Ilelah)