Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-17 11:20:43    
Rawar daji ta "Zaman Lafiya a 2007" tana da muhimmiyar ma'ana

cri

A ran 16 ga wata, jagoran ofishin cudanya da kasashen waje a ma'aikatar tsaron kasar Sin ya gaya wa kafofin watsa labaru cewa, rawar daji mai suna "Zaman Lafiya a 2007" da dakarun kasashen kungiyar hada kai ta Shanghai za su yi cikin hadin guiwa domin fama da ta'addanci tana da muhimmiyar ma'ana kuma za ta yi tasiri a nan gaba.

Wannan jagora ya nuna cewa, wannan rawar daji wani muhimmin mataki ne da kasashen kungiyar hada kai ta Shanghai suka dauka domin fama da sabbin barzana da kalubale domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da neman bunkasuwar yankin da suke ciki. Shi kuma wani muhimmin mataki ne da suka dauka domin yin yaki da 'yan ta'addanci da masu yunkurin kawo baraka da masu tsattauran ra'ayi. Wannan rawar daji ta kuma bayyana cewa, yanzu hadin guiwar da ake yi a tsakaninsu ta fuskar tsaron kansu ta riga ta kai wani sabon mataki. Wannan kuma ya bayyana cewa, kungiyar hada kai ta Shanghai tana da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali har da raya wata duniyar da ke cike da jituwa. (Sanusi Chen)