|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2007-07-17 09:25:59
|
An rufe taron kasa da kasa kan batun Darfur a Libya
cri
Ran 16 ga wata, a birnin Tripoli, hedkwatar kasar Libya, an rufe taron kasa da kasa kan batun yankin Darfur na kasar Sudan. Wakilin musamman na kasar Sin Liu Guijin mai kula da batun Darfur ya halarci taron, inda ya bayyana ra'ayi da matsayin da kasar Sin ke tsayawa a kai kan daidaita batun Darfur.
Mr. Liu ya yi nuni da cewa, ya kamata Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU da Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin Sudan su taka muhimmiyar rawa don sa kaimi kan daidaita wannan batu ta hanyar siyasa. Kamata ya yi bangarori daban daban da abin ya shafa su ba da kyakkyawan tasiri kan kungiyoyin 'yan hamayya da ke Darfur domin maido da shawarwarin siyasa da gwamnatin kasar cikin sauri, sa'an nan kuma su ba da taimako a fannin jin kai da samun bunkasuwa.(Tasallah)
|
|
|