Labarin farko shi ne akwai wuraren addinai fiye da 1700 a jihar Tibet. Kwanan baya, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya wani taron manema labaru, inda aka bayar da labari cewa, ya zuwa yanzu akwai wuraren addinai fiye da 1700 a jihar Tibet mai cin gashin kanta. Ana tafiyar da harkokin addinai iri iri kamar yadda ya kamata.
An bayyana cewa, yawancin mutanen kabilar Tibet suna bin addinin Buddha, sannan yawan mutanen da suke bin addinin Musulunci ya kai dubu 2 yayin da mutane kimanin dubu 6 suke bin addinin Katolika. Sabo da haka, harkokin addinai da ake yi a jihar Tibet suna jawo hankulan masu yawon shakatawa sosai.
Labari daban shi ne, za a yi gasar tafiye-tafiye da kafa ta kasa da kasa ta Nam Co ta karo ta biyu a jihar Tibet
A kwanan baya, kwamitin shirya gasar tafiye-tafiye da kafa ta kasa da kasa ta Nam Co ta karo ta biyu ta jihar Tibet ya soma gayyatar wadanda suke da sha'awar yin tafiye-tafiye da kafa na kasa da kasa domin halartar gasar yin tafiye-tafiye da kafa ta Nam Co ta karo ta biyu da za a yi tun daga ran 4 zuwa ran 10 ga watan Agusta a jihar Tibet.
Bisa shirin da aka tsara, wadanda za su halarci wannan gasa za su tashi daga fadar Potala da ke birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet zuwa tafkin Nam Co da ke arewacin jihar. Wadanda za su halarci wannan gasa za su yi ta yin tafiye-tafiye da kafa daga kilomita 10 zuwa kilomita 15 a kowace rana. A waje daya, za su ratsa bakin wani babban dutsen da tsayinsa ya kai mita 5200 daga leburin teku.
A ganin 'yan kabilar Tibet, tafkin Nam Co yana matsayin farko daga cikin tafkuna masu tsarki 3 na jihar Tibet. Kwatancin wannan tafki ya yi sama da 4718 daga leburin teku. A cikin tafkunan da fadin kowanensu ya kai fiye da murabba'in kilomita dubu 1, kwatancin tafkin Nam Co ya fi tsayi daga leburin teku.(Sanusi Chen)
|