Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-13 16:23:02    
Beijing na sanya kokari matuka wajen tabbatar da hasashen " taron wasannin Olympic na kore-shar"

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da, cewa manyan hasashe iri uku wato na " taron wasannin Olympic na zamantakewar al'adu da kimiyya da fasaha da kuma na kore-shar" sun rigaya sun shiga cikin zukatan jama'ar kasar Sin. Babu tantama, wadannan manyan hasashe uku suna wakiltar fahimta da kuma kishin zuciya da jama'ar kasar Sin ke nuna wa ra'ayin Olympic. Amma ba za a iya samun sauki wajen tabbatar da wadannan manyan hasashe uku ba. Musamman ma tabbatar da hasashen " taron wasannin Olympic na kore-shar", wani babban kalubale ne ga gwamnatin birnin Beijing.

Domin kokarin gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a cikin wani kyakkyawan muhalli na zaman lafiya da kuma kyautata gurbataccen halin da birnin Beijing take ciki bisa kyakkyawar damar mai ma'anar tarihi da aka samu ta shirya taron wasannin Olympic, gwamnatin birnin ta zuba makudan kudade da samar da leburori da kuma kayayyaki tun bayan da aka soma gabatar da rokon daukar bakuncin taron wasannin Olympic na shekarar 2008.

A gun wani taron ganawa da manema labaru da aka shirya kwanakin baya a nan birnin Beijing game da maganar kiyaye muhalli, Mr. Shi Hanmin, shugaban hukumar kiyaye muhalli ta birnin Beijing ya bayyana, cewa: " Tun daga shekarar 1998, kudaden da muka kashe wajen kyautata muhalli kalilan ne, wadanda yawansu ya kai kudin Sin Yuan biliyan goma kawai a kowace shekara; Amma a wadannan shekaru biyu da suka gabata, mun kara zuba kudade da yawansu ya kai Yuan biliyan ashirin da biyar. A wannan shekara ma zai karu karuwar gaske".

Alkaluman sun yi nuni da, cewa ingancin yanayin sararin samaniya na birnin Beijing ya samu kyautatuwa cikin shekaru 8 a jere da suka shige, wato ke nan lokutan kyakkyawan yanayin sama da aka samu sun karu zuwa 241 a shekarar bara daga kwanaki 100 a shekarar 1998; Ban da wannan kuma, ana iya samar da ruwan sha mai tsabta ga bainal jama'a; dadin dadawa, a galibi dai, an samu ci gaba wajen rage hayaniya da kuma iska mai guba da akan samu a birnin. " Amma duk da haka", in ji shi," har ila yau dai ayyukan kiyaye muhalli na taron wasannin Olympic na fuskantar kalubale a shekara daya da 'yan watanni kawai da suka yi saura don gudanar da shi. Babban kalubale na farko, shi ne karuwar ababen hawa ,wadanda yawansu ya karu zuwa miliyan uku a wannan shekara. Lallai masu shirya taron wasannin Olympic na Beijing sun nuna halin zuciya mai sarkakiya game da wannan. Mataimakin mai garin Beijing Mr. Ji Lin ya furta, cewa karuwar ababen hawa na alamanta wadatuwar tattalin arziki da kyautatuwar zaman rayuwar mazauna birnin yayin da yake janyo cunkuso ga zirga-zirga da kuma kazamcewar muhalli.

Amma duk da haka, mahukuntan gwamnatin birnin Beijing ba za su yi tsammanin daukar matakin kayyade karuwar motoci don warware wannan magana ba. Bayan da suka yi nazarin fasahohin da sauran birane masu masaukin taron wasannin Olymmic suka samu, sun gano cewa, hanya mafi kyau da akan bi, ita ce dakatar da tuka motoci cikin gajeren lokaci. Alal misali: a lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic na Atlanta a shekarar 1996, an dakatar da tuka motoci da yawansu ya kai miliyan biyu da dubu dari biyar; kuma a lokacin da ake gudanar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika a shekarar bara a nan birnin Beijing, an dakatar da tuka motoci da yawansu ya kai dubu dari tara. Yanzu, wasu kwararru suna kiyasta motoci nawa ne da za a dakatar da tuka su a duk tsawon lokacin taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai kamawa.

Ko da yake matakinn nan da za a dauka zai iya kyautata ingancin iskar sararin samaniya, amma kuwa ba zai iya sauya muhalli daga doron kasa ba. Game da wannan dai, sassan da abun ya shafa na birnin Beijing za su kara kyautata ingancin mai da kuma yin kwaskwarimar wasu gidajen mai da ba su isa biyan bukatu ba.

A karshe dai, Mr. Ji Lin ya fada wa manema labaru, cewa gwmnatin birnin Beijing za ta sauke alhakin dake bisa wuyanta na bada tabbaci ga samun kyakkyawan ingancin iska a lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing. Ko shakka babu, gwamnatin birnin Beijing za ta rubanya kokari wajen cika alkawarin da ta dauka da kuma tabbatar da hasashen " taron wasannin Olympic na kore-shar".