Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-13 10:55:02    
Korea ta Kudu ta samar wa Korea ta Arewa mai mai nauyi

cri

Jiya Alhamis, a nan birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mr. Qin Gang ya shelanta cewa, shawarwarin tsakanin bangarori shida a zagaye na shida ya tsaida kudurin kiran taron shugabannin kungiyoyin wakilai daga ran 18 zuwa 19 ga watan da muke ciki a nan Beijing. A lokaci daya, bisa abubuwan a aka tanada cikin " takardar hadin gwiwa ta ran 13 ga watan Fabrairu" da aka fito da shawarwarin tsakanin bangarori shida kan batun nukiliyar Zirin Korea, jiya dai, Korea ta Kudu ta yi jigilar mai mai nauyi na Ton 6,200 na kashin farko zuwa Korea ta Arewa. Wasu manazarta sun yi hasashen cewa, wannan dai wani muhimmin mataki ne da aka dauka don daidaita wannan batu kamar yadda ya kamata.

Takardar hadin gwiwar ta tanadi cewa, ya kamata Korea ta Arewa ta rufe na'urorinta na nukiliya a Yongbyon da kuma gayyaci sufetocin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya don su sake koma wa Korea ta Arewa, sa'annan Korea ta Kudu ta samar Korea ta Arewa mai mai nauyi da yawansu ya kai Ton 50,000. Ana kyautata zaton cewa,jirgin ruwa mai daukar mai na Korea ta Kudu zai sauka tashar ruwa ta Seonbong na Korea ta Arewa a ran 14 ga wata. Bisa yarjejeniyar da bangarorin biyu wato Korea ta Kudu da Korea ta Arewa suka daddale. Sauran mai mai nauyi da suka rage, za a kuma kammala jigilarsu duka-duka kafin ran 1 ga watan gobe.

Bayan da aka janye haramcin da aka sanya wa Korea ta Arewa wajen yin amfani da kudaden da ta ajiye a bankin BDA na Macao, gwamnatin Korea ta Arewa ta dauki jerin matakai a 'yan kwanakin baya don aiwatar da " Takardar hadin gwiwa". A ran 21 ga watan da ya gabata, mai bada taimako ga sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka bugu da kari jagoran tawagar wakilan kasar a shawarwarin tsakanin bangarori shida kan batun nukiliyar Korea ta Arewa ya ziyarci Korea ta Arewa bisa gayyatar da aka yi masa, inda bangarorin biyu suka amince da aiwatar da " Takardar hadin gwiwa", da kuma cimma daidaito kan kiran taron shugabannin kungiyoyin wakilai a shawarwarin tsakanin bangarori shida kan batun nukiliyar Korea ta Arewa da kuma taron ministocin harkokin waje na bangarorin shida ba tare da bata lokaci ba. Game da batun gudummowar mai mai nauyi da za a bayar, Korea ta Arewa ita ma ta nuna saukin kai cewa, domin daukaka ci gaban yunkurin shawarwarin tsakanin bangarori shida, za ta rufe na'urorinta na nukiliya a Yongbyon da zarar ta ta samu mai mai nauyi na kashin farko da aka yi jigilar ba wai sai bayan ta samu dukan mai na nauyin Ton 50,000 ba.

Ban da wannan kuma, bisa abubuwan da aka tanada cikin " takardar hadin gwiwa", Korea ta Arewa ta kuma gayyaci tawagar wakilan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya don ta kai ziyara a kasar. Bangarorin biyu sun samu ra'ayi daya kan batun rufe na'urorin nukiliya na Yongbyon. Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, Mohammed El-Baredei ya sa ran alherin cewa, za a iya rufe dukan na'urorin nukiliya a Yongbyon wata daya bayan da gwamnatin Korea ta Arewa ta soma aiwatar da wadannan matakai. Wata kungiyar bincike ta hukumar kula da makamshin nukiliya ta duniya ta tashi jiya zuwa Korea ta Arewa don sa ido kan ayyukan rufe na'urorin nukiliya da gwamnatin kasar za ta yi.

Mr. Qin Gang ya lashi takobin cewa, bangaren kasar Sin zai sanya kokari tare da sauran bangarori daban-daban wajen cimma tudun dafawa a gun taron shugabannin kungiyoyin wakilai da za a gudanar.

A wata sabuwa kuma, an ce, kasashen Amurka, da Korea ta Kudu da kuma Rasha da dai sauransu sun yi bege ga wannan taro, inda za a tattauna yadda za a aiwatar da matakai na nan gaba da kuma gudanar da taron ministocin harkokin waje na bangarori shida, ta yadda za a gaggauta yunkurin haramta kasancewar makaman nukiliya a Zarin Korea. (Sani Wang )