
BEIJING. A ranar 12 ga wannan wata, sashen kula da ayyukan bukatun yau da kullun na sojin kasar Sin ya umurci dukkan rundunoninsa da su dauki matakan samar da ingantaccen abinci a yayinda ake ta karin samun barazana kan harkokin kiwon lafiya.
A cikin wata sanarwar da sashen ya rarraba, an bukaci dukkan kwamandoji su fahimci cewar ingantaccen abinci yana da muhimmanci ga rundunar sojin jama'a ta kasar Sin domin kasancewarsu cikin shirin ko ta kwana.

Dole ne dukkan kananun sassa su sa ido kan abinci tun daga sayensa har zuwa lokacin sarrafa shi, kuma an haramta yin amfani da kayayyakin abinci na jabu ko kuma marasa inganci.
Tilas ne a bayar da muhimmanci ga sa ido kan ingancin abincin sojoji kuma tilas ne yan kwangila su yi la'a kari da hakan.(ilelah)
|