Kamar yadda muka gaya muku lardin Henan wani lardi ne dake gabashin kasar Sin ta tsakiya.Bayan da kasar Sin ta aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen ketare da kawo sauyi,lardin Henan ba a bar shi a baya ba.Gwamnatin lardin Henan ita ma ta mai da hankali wajen bin manufar,har ma ta tsara nata shiri na shiga da abubuwa na zamani daga gabas da sayar da abubuwa a bangaren yamma na kasar Sin.Jimlar kudin da lardin ya samu wajen cinikin fici da shigi ta kai dalar Amurka miliyan 4716,daga ciki kudin da aka samu wajen fitar da kayayyaki ya kai dalar Amurka miliyan 2980,dukkansu sun kai matsayin koli a tarihi.gwamnatin lardin ta kuma kara kyautata shirye-shiryenta na fitar da kayayyakin ciniki zuwa ketare,ta maye gurbin fitar da alkama zuwa ketare wanda a da babu wani lardi na kasar Sin ya fitar da alkama zuwa ketare,ta kuma fara fitar da naurori da injuna da kayayyaki na zamani zuwa ketare.
Ta kuma gina wata tashar jirgin kasa ta gabas da filin jirgin sama a birnin Zhengzhou,wurare biyu na mafita ga lardin zuwa ketare.Kasashe da bangarorin da suka yi ciniki da lardin Henan na kasar Sin sun wuce 160.Fagagen da aka yi amfani da kudaden ketare n kara habakawa,ingancin kayayyakin da aka kera na kara karuwa.Manyan kamfanoni na kasa da kasa 24 daga kamfanoni mafi cigaba a duniya sun gina sassansu bi da bi a wannan lardin kamar su kamfanonin Hitachi da Toshiba da Phillip da Pricemart da Man na Jamus.
Wasu masana'antu na lardin sun shiga takara a kasuwannin duniya ta hanyar ba da hadin kai da kera kayayyakin da kamfanonin ketare ke bukata.Masana'antu sama da hamsin sun tafi kasashen ketare sun kafa nasu sassa ko zuba jari wajen kafa masana'antu.Wajen aiwatar da shirin shiga da abubuwa daga gabas da sayar da kayayya a bangaren yamma na kasa,lardin Henan ya hada kansa da lardin Guangdong da birnin Shanghai wajen tattalin arziki da ciniki,haka kuma ya hada kansa da mashahuran manyan makarantu da cibiyoyin binciken ilimin kimiyya na kasar Sin kamar Jami'ar Peking da Jami'ar Tsinhua da cibiyar nazarin ilimin kimiyya ta kasar Sin.lardin ya yi nasarar shirya bikin baje na kayayyakin da aka kera a lardin a birnin Lanzhou dake yammancin kasar Sin da tattaunawar cinikayya a birnin Urumuchi da shawarwari kan zuba jari a jihar Guangxi da makamantansu,ta haka kuma kasuwannin da kayayyakin da ake kera a lardin Henan na kara habaka a yammancin kasar Sin.Har ma wasu masana'antun lardin Henan sun fara saye kamfanoni ko kafa masana'antu a yammancin kasar Sin.
Lardin Henan ya kuma samu babban cigaba wajen kimiyya da fasaha da kuma ilimi da zamantakewa.Ya nuna kwazo da himma wajen tafiyar da manufar bunkasa lardin Henan ta hanyar kimiyya,ya kara kwarewar kwararru wajen binciken ilimin kimiyya.Da akwai kwararru na musamman miliyan daya da dubu dari hudu da hukumomin nazari da bunkasa fasaha fiye da 1300.An mai da sakamakon binciken kimiyya abun dake iya amfani da su da su dau kashi 35 bisa dari.Cigaban kimiyya da fasaha ya daukaka cigaban tattalin arziki da kashi 43 bisa dari.Ilimin na samu saurin yaduwa.Yaran da shekarunsu ya isa shiga makarantun firamare kusan kashi dari bisa dari sun shiga.yaran da shekarunsu ya isa shiga makarantun junior sakandare kashi 97 bisa dari sun shiga,shirin ba da ilimi kyauta na shekaru tara ya shafi kashi 93 bisa dari na mutanen lardin.lalle lardin nan ya kama gaba wajen samar da ilimi a makarantun firamare.Makarantun senior sakandare ma na karuwa da sauri.manyan makarantu a lardin su ma suna karuwa.A shekara ta 1997 da akwai manyan makarantu 50 a halin yanzu sun kai 66,daliban dake cikin manyan makarantu sun karu daga dubu 136 a shekara ta 1997 zuwa dubu 557 a halin yanzu wato sun karu da ninki 3 da digo daya.Lardin nan ya zarce matsakaicin matsayi na duk kasa wajen daukar daliban manyan makarantu. (za a cigaba)
|