Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-11 18:10:57    
Gidan rediyon kasar Sin wato Chana Radio International ya yi kokarin kafa sabbin kafofin yada labarai

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gidan rediyon kasar Sin ya sauya sifarsa na aiwatar da harkokin yada labarai ta hanyar gargajiya, kuma tana aiwatar da ayyukan yada labarai ta hanyar sabbin kafofin yada labarai cikin himma da kwazo, yana ta kara ba da karfin tasirinsa a wajen ra'ayoyin jama'a na duk duniya. Kwanan baya, ba da dadewa ba, shugaban gidan rediyon kasar Sin wato shugaban gidan CRI Mr Wang Gengnian ya karbi ziyarar da tashar internet mai suna "China On Line" da tashar internet mai suna "People" suka kawo masa, inda ya bayyana sosai kan manyan tsare-tsare da gidan rediyonsa ya tsara wajen raya al'adu da sabbin kafofin yada labarai.

Jama'a masu sauraro, gidan rediyon kasar Sin na da tarihin da ya kai shekaru 65, a kowace rana, yana watsa labarai da harsuna 43 na gida da na waje zuwa kasashe da jihohi fiye da 200 na duniya. Shi ne gidan mai farin jini a duniya. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, bisa albarkacin samun bunkasuwar kimiyya da fasaha, gidan rediyon kasar Sin ta yi himmar raya harkokin sabbin kafofin yada labarai a yayin da ya ke watsa labaru ta hanyar gajeren zango?

A ganin shugaban gidan rediyon kasar Sin Mr Wang Gengnian, kodayake samun sabbin kafofin yada labarai ya kawo wa kafofin yada labarai ta hanyar gargajiya babbar lambar matsi, amma kafofin yada labarai ta hanyar gargajiya sun iya samun bunkasuwa ta hanyar yin amfani da sabbin kafofin yada labarai, ya bayyana cewa, mun fahimci sosai cewa, idan kafofin yada labarai ta hanyar gargajiya suka sami sabbin fasahohi, to karfin rayuwarsu zai kara ingantawa, alal misali, gidan rediyon kasar Sin yana watsa labarai ta hanyar gargajiya cikin shekaru 65, kodayake ana kiran gidan rediyonmu da gidan muryar Amurka da kamfanin BBC da cewar wai manyan gidajen rediyo guda uku ke nan a duniya wajen yin amfani da harsuna da yawan tsawon lokutan yada labarai da sauransu, amma tasirin da gidanmu ya yi ba ya da karfi, amma bayan mun yi amfani da sabbin kafofin yada labarai, sai gidanmu ya sami bunkasuwa da saurin gaske a cikin shekarun nan biyu da suka wuce. A cikin shekarun biyu ko fiye da suka wuce, mun tsaya bisa matsayin farko a duniya a fannin watsa labaru ta rediyo da harkokin Internet, wato gidan rediyonmu ya zauna da gindinsa bisa na BBC da gidan muryar Amurka, wannan dai sauyawar da aka samu ta hanyar yin amfani da sabbin fasahohi.

Game da sabbin kafofin yada labarai, an bayyana cewa, ta hanyar yin afmani da fasahar internet da sauran sabbin fasahohi, wadanda sabbin kafofin yada labarai suke amfani da su sun sami sauye-sauye, yanzu ana cewa, sabbin kafofin yada labarai suna kunshe da kafofin yada labarai na Internet da IPTV da rediyo na salula da rediyo mai hoto na salula da dai sauransu.Bisa albarkacin samun bunkasuwar fasahohi, za a iya kara samun sauran hanyoyin yada labarai.

A shekarar 1998, gidan rediyon kasar Sin ya soma kafa tashar internet mai suna "CRI On Line", kuma ta bude tashoshinsa na internet ta hanyar yin amfani da harsuna Sinanci da Ingilish da Faransanci da Jamusanci da harshen Spain , wato harsuna 5 ke nan, daga nan sai gidan rediyon kasar Sin ya kara samun bunkasuwa wajen kafa sabbin kafofin yada labarai. Mataimakin babban edita kuma direktan cibiyar shirye-shiryen kafofin yada labarai na gidan rediyon kasar Sin Mr Ma Weigong ya bayyana cewa,

(yinxiang 3)

bisa albarkacin samun bunkasuwar kimiyya da fashohi, musamman ma bisa albarkacin samun tashoshin internet da sauran sabbin kafofin yada labarai, mun fahimci cewa, idan ba mu samu bunkasuwa da sauri sosai tare da saurin bunkasuwar sabbin kafofin yada labarai ba, to tabbas ne za mu sami cikas wajen ci gaba da kasancewarmu da samun bunkasuwarmu. Ayyukan da muke yi sun hada da aiwatar da harkokin rediyo ta hanyar internet da dai saruansu. Yanzu, tasirin gidan rediyonmu ya kara karfi. Ra'ayin shugaban gidan rediyon kasar Sin yana daya da na duk ma'aikatansa, kuma manyan tsare-tsare na al'adu da sabbin kafofin yada labarai na gidan rediyon kasar Sin tabbas ne za su sa kaimi ga yada al'adun kasar Sin a duniya da kuma kara wa duniya fahimtar kasar Sin.(Halima)