Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-11 17:26:52    
Haikalin Yasukuni, wurin ibada ne ga masu ra'ayin nuna karfin soja

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Sanusi Isah Dankaba, mai sauraronmu a ko da yaushe, wanda ya fito daga birnin Keffi da ke jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya. Sanusi ya sha turo mana tambayoyinsa, kuma a cikin wata wasikar da ya turo mana a kwanan baya, ya ce, a duk lokacin da shugabannin kasar Japan suka kuduri ziyarar makabartar Yasukuni, sai ka ji wata cece kuce ta tashi tsakanin Japan da Sin da kuma wadansu kasashe na Asiya, don Allah mene ne ya haddasa wannan lamari tun da can? Bayan haka, tarihi ya nuna mana cewa, Japan ta taba mamaye wadansu yankuna na kasar Sin a lokacin yakin duniya na biyu, to, don Allah, ina son in san wadanne yankuna ne kasar Japan ta mamaye daga cikin yankunan kasar Sin, sa'an nan, kamar kimanin mutane nawa ne suka rasa rayukansu?

Tun daga shekarun 1870, Japan ta yi ta kai hare-hare ga Sin da Koriya da dai sauran kasashen Asiya, don neman kafa mulkin mallaka a kasashen Asiya. A shekarar 1931, maharan Japan sun mamaye larduna uku da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Sa'an nan a ranar 7 ga watan Yuli na shekarar 1937, sojojin Japan sun kai hari ga sojojin kasar Sin da ke Lugouqiao, wani wurin da ke kudu maso yammacin birnin Beijing. Daga nan ne kuma, yakin kin maharan Japan na tsawon shekaru takwas ya barke daga dukan fannoni a tsakanin jama'ar Sin da maharan Japan. Hare-haren maharan Japan sun kasance babbar masifa ga jama'ar kasar Sin. Sakamakon hare-haren, Japan ta mamaye larduna 26 tare da gundumomi da garuruwa sama da 1500 daga yankunan kasar Sin, a yayin da sojoji da fararen hula na kasar Sin sama da miliyan 35 suka mutu ko kuma ji raunuka, sa'an nan, Sin ta kuma yi hasarorin da yawansu ya kai dallar Amurka biliyan 600 a fannin tattalin arziki.

To, mun dai dan tabo magana kan tarihin hare-haren da Japan ta kawo wa kasar Sin, yanzu bari mu koma kan batun haikalin Yasukuni. Haikalin Yasukuni ya kasance wani wurin ibada ne ga masu ra'ayin nuna karfin soja na Japan, A nan wurin, ana bauta wa wadanda suka mutu a yake-yake, musamman ma a hare-haren da Japan ta kai wa kasashen waje.

An kafa haikalin Yasukuni ne a shekarar 1879. Kasancewar haikalin a birnin Tokyo, babban birnin kasar Japan, fadinsa ya kai muraba'in mita sama da dubu 100. A bakin kofar haikalin Yasukuni, akwai hasumiyoyi biyu masu tsayin mita kimanin goma, wadanda aka yi sassaka a jikinsu, kuma sassaka da aka yi a jikinsu sun nuna yabo kan hare-haren da Japan ta kawo wa kasar Sin, misali yadda Japan ta mamaye lardin Taiwan na kasar Sin a shekarar 1895 da kuma arewa maso gabashin kasar a shekarar 1931 da hare-haren da ta kawo wa kasar duka sun zama abubuwan tarihi da ake ji alfaharinsu a wurin.

A babban dakin haikalin kuma, ana bauta wa sojoji da yawa da suka mutu a hare-haren da Japan ta kai wa kasashen waje. A watan Oktoba na shekarar 1978, an kuma ajiye allunan da aka rubuta sunayen manyan masu aikata laifuffukan yaki 14, da dai sauran masu laifuffukan yaki sama da dubu biyu a ciki, don a bauta musu a matsayin wadanda suka sadaukar da rayukansu ga kasarsu.

Sa'an nan, a cikin haikalin Yasukuni, akwai kuma wani gidan nune-nune, inda aka nuna kayayyakin da sojojin Japan suka yi amfani da su wajen kisan gilla da kuma wasu makamansu a lokacin yakin duniya na biyu, kuma nune-nunen suna neman halaltar da hare-haren Japan, suna kokarin halaltar da hare-haren da Japan ta kawo wa kasar Sin. A can wurin, akwai kuma hotunan manyan masu laifuffukan yaki su 14 da aka manne a jikin bango, don a bauta musu.

To, Sanusi da ma sauran masu sauraronmu, watakila yanzu kun gane, me ya sa Sin da sauran kasashen Asiya su kan nuna adawa ga ziyarar da shugabannin Japan suka kai wa haikalin Yasukuni, sabo da a ko yaushe kuma duk wanda ya kai ziyara ga haikalin Yasukuni, abin zai zama wulakanci da cin fuska ga jama'ar Asiya wadanda suka sha fama da ta'asar masu ra'ayin nuna karfin soja na Japan. Kasancewar haikalin Yasukuni wuri ne na yada ra'ayin nuna karfin soja, a hare-haren da Japan ta kai wa sauran kasashe, masu ra'ayin nuna karfin soja sun yi amfani da haikalin Yasukuni wajen karfafa gwiwar sojojinta, bayan yaki kuma, haikalin ya ci gaba da kasancewa wurin ibada ga masu ra'ayin nuna karfin soja.

Jama'ar Asiya, ciki har da jama'ar Sin, har kullum, suna tsayawa tsayin daka kan kin yarda da shugabannin Japan da su kai ziyara a haikalin Yasukuni, a ganinsu, ziyarar da suka kai wa haikalin ya bayyana matsayin da suka dauka kan hare-haren da Japan ta taba kai wa kasashen Asiya, wadda kuma ta nuna hanyar da za ta bi a nan gaba. Gwamnatin kasar Sin kullum tana ganin cewa, huldar da ke tsakaninta da Japan ba za ta iya bunkasa yadda ya kamata ba, muddin dai Japan ta kula da tarihi yadda ya kamata, kuma hakan nan dai, Japan za ta iya samun amincewa daga kasashen Asiya da ke makwabtaka da ita da kuma gamayyar kasa da kasa, hakan nan kuma ya dace da babbar moriyar jama'ar Japan.(Lubabatu)