Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-11 08:26:11    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (03/07-10/07)

cri

Ran 4 ga wata,a gun cikakken taro na 119 na kwamitin wasannin Olimpic da aka yi a birnin Guatemala na kasar Guatemala,shugaban kwamitin Jacques Rogge ya sanar da cewa,birnin Sochi na kasar Rasha ya samu ikon shirya taron wasannin Olimpic na yanayin sanyi na shekarar 2014,wannan shi ne karo na farko da kasar Rasha ta samu damar shirya taron wasannin Olimpic na yanayin sanyi.

Ran 3 ga wata,aka kammala zama na 5 na gasar cin kofin shugaban kasar Rasha ta wasan kwallon raga na mata a birnin Yekaterinburg na kasar.A gun zagaye na karshe na gasar,kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Holand da 3 bisa 1 kuma ta zama zakarar wannan gasa.Aka kafa gasar cin kofin shugaban kasar Rasha ne a shekarar 2003 bisa shawarar da tsohon shugaban kasar Rasha Boris Yeltsin ya ba da.Yanzu ta riga ta zama gasar gargajiya ta wasan kwallon raga ta mata a duniya.Gaba daya kungiyoyi 8 da suka hada da kungiyar kasar Sin da ta Rasha da ta Holand da ta Turkey da ta Japan sun hallarci wannan zama na gasar da aka shirya.

Ran 8 ga wata,aka kammala budaddiyar gasar kwallon tennis ta Wimbledon ta wannan shekarar da muke ciki.A gun zagaye na karshe na gasar maza,`dan wasa daga kasar Switzerland Rogger Federer ya lashe `dan wasa daga kasar Spain Rafael Nadal da 3 bisa 2,ya zama zakaran maza.Wannan shi ne karo na biyar da Federer ya zama zakaran maza na gasar kwallon tennis ta Wimbledon.Kafin wannan,a gun zagaye na karshe na gasar mata,`yar wasa daga kasar Amurka Venus Williams ta lashe `yar wasa daga kasar Faransa Marion Bartoli da 2 bisa 0,ta zama zakarar mata.(Jamila zhou)